Jam’iyyar APC mai mulki ta dage babban taronta da ta shirya gudanarwa a radar 26 ga watan Febrairu har illa Masha Allah.ABUJA,.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Fabrairu na shekarar 2022.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe da Sanata John James Akpanudoedehe ne dai suka sanar da hakan a cikin wasikar da suka aikewa hukumar zabe zai zaman kanta ta Najeriya wato INEC a bisa wannan sabon mataki da jam’iyya ta dauka.
A cikin wasikar, jam’iyyar APC ta ce wannan sanarwar ta shawo gaban sanarwar da jam’iyyar ta fitar tun farko a kan babban taron kasa mai suna APC/NHDQ/INEC/019/22/14 wanda jam’iyyar ta dogara ne kan kimanta kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Haka kuma, sanarwar jam’iyyar APC ta dogara ga sashe na 85 na dokar zabe ta shekarar 2010 kamar yadda aka yiwa gyarar fuska da kuma bin sashe na 12 sakin sashi na 6 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta APC, Jam’iyyar ta aikawa hukumar zabe ta INEC sanarwa cewa za ta gudanar da taronta na shiyya-shiyya a ranar asabar 26 ga watan Maris na shekarar 2022.
Jam’iyyar ta kuma bukaci hukumar INEC ta shirya tura jami’anta don aikin sa ido kamar yadda doka ta tanadar a yayin da jam’iyyar ke fatan samun hadin kan INEC.
Hakazalika, jam’iyyar APC ba ta sanar da wata ranar babban taron ba sai dai wasu majiyoyi daga sakatariyar jam’iyyar da suka bukaci a sakaya sunansu sun bayyana cewa akwai yiyuwar jam’iyyar ta gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Maris mai zuwa.
An dai dade ana kai ruwa rana kan batun shirya baban taron jam’iyyar mai mulki wanda a da, aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2022, amma batutuwan da suka hada da tsarin raba kujeru zuwa shiyya-shiyya da rikice-rikice da aka fuskanta a jam’iyyar APC a matakin jihohin na zama barazana.
Idan ana iya tunawa, wannan ba shi ne karon farko da jam’i da rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa da kulle kulle tsakanin jiga-jigan jam’iyyar ta APC.