Sojojin Najeriya sun daƙile kwanton ɓaunar da ISWAP suka yi a Borno

Rundunar Operation Hadin Kai wadda ke ƙarƙashin sojin Najeriya ta daƙile wani yunƙuri na harin kwanton ɓauna kan wasu motoci a kan hanyar Bama da ke Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa mayaƙan ISWAP ne suka buɗe wuta a manyan hanyoyin Jihar Borno biyu Rahotanni sun ce tun da farko mayaƙan sun saka shingaye da dama a kwanar garin Banki domin garkuwa da fararen hula a Ƙaramar Hukumar Bama a ranar Asabar.

Wani babban kwamanda ya shaida cewa dakarun da ke shawagi domin tabbatar da tsaro a yankin ne suka daƙile hare-haren masu iƙirarin jihadin jim kaɗan bayan an kira su a waya an shaida musu halin da ake ciki.

Kwamandan ya bayyana cewa mayaƙan ISWAP ɗin waɗanda suke riƙe da wasu matafiya a kan hanya, sun gudu bayan ganin sojojin inda suka bar waɗanda suka kama.

Ya bayyana cewa harbin bindiga da mayaƙan suka yi, ya yi sanadin fashewar gilasan baya na motocin matafiyan amma babu wanda ya rasu.

A ɗayan ɓangaren kuma, dakarun bataliya ta 152 a yayin da suke shawagi a kan hanyar Bula Yobe – Darel Jamel a ranar dai ta Asabar sun daƙile wani harin mayaƙan na ISWAP.

Haka kuma sojojin na Najeriya bakwai ne suka tsallake rijiya da baya a sakamakon nakiya da ƴan ISWAP suka dasa musu a hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

More from this stream

Recomended