
Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe wani kwamshina a jihar Katsina a arewacin Najeriya.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema labarai a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da daddare.
Sannan wasu rahotannin daga jihar Neja a arewa ta tsakiyar ƙasar kuma ƴan bindigar sun kashe mutum 16 a masallaci wasu goammai kuma sun jikkata a wani hari da ‘aka kai ƙauyen Ba’are a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Nejan.
Ahmed Ibrahim Matane shi ne sakataren gwamnatin jihar ta Neja, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Laraba.