‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya Bakwai A Katsina – AREWA News

Da yammaci yau ne, da misalin karfe biyar, ‘yan bindigar dauke da bindigogi, sun tare hanyar Jibia, sun sace wadansu matafiya guda bakwai, akan hanyar su ta zuwa garin Gurbi daga karamar hukumar Jibia, dukkan su maza ne, amma sun bar mace daya sakamakon ba ta iya tafiya tana da juna biyu.

Majiyar RARIYA ta tabbatar mata cewa an tare matafiyan nan yau, suna cikin motar su kirar Golf a dai-dai dajin Dogan Karfe, kusa da garin Tsayau da ke cikin karamar hukumar Jibia, kuma sun shiga daji da su. Karamar Hukumar Jibia na cikin Kananan Hukumomi da ke fama da matsalar ‘yan bindigar. Mutanen dukkan su yan garin Gurbi ne, kuma yan kasuwa ne.

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari yana mahaifarsa ta garin Daura, domin yin hutun mako daya. Ranar juma’a da ta gabata ne, aka sace daliban makarantar sakandire ta Kankara, inda sama da daliban dari ukku da talatin da ukku na hannun su.

Allah ya bayyanar da su!

More from this stream

Recomended