An yi waje da Man United a Champions League na bana

RB Leipzig

Manchester United ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gidan RB Leipzig a gasar Champions League ranar Talata a Jamus.

Cikin minti 13 aka zura kwallo biyu a ragar United ta hannun Angelino da kuma Amadou Haidara.

A minti na 69 ne Justin Kluivert ya kara kwallo na uku a ragar Manchester United.

Sai a min 80 United ta fara sa kwazo ta zare kwallo daya ta hannun Bruno Fernandes a bugun fenariti, kuma minti biyu tsakani Paul Pogba ya zare na biyu.

United wadda ya kamata ta yi canjaras domin zuwa mataki na biyu ta koma ta uku a cikin rukuni da maki tara.

RB Leipzig ce ta zama ta daya a rukunin na takwas da maki 12.

Kungiyar ta Old Trafford za ta koma buga gasar Europa League, kofin da ta lashe a kakar 2017.

More from this stream

Recomended