Coronavirus: PDP ta bukaci a yi bincike kan mutuwar mutane a Kano

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kano na karkashin dokar kulle

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci a gudanar da bincike kan mutuwar jama’a da dama a Kano, inda ta ce akwai bukatar shugaban kasa ya kai ziyara a can.

Jami’yyar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce rahotanni sun nuna cewa daruruwa mutane sun rasu cikin mako guda Kano ba tare da sannin abin da yayi sanadiyyar mutuwarsu ba.

Kiran na zuwa ne a lokacin da ake samu rahotanni masu cin karo da juna kan abin da ya janyo mutuwar jama’a a Kano a lokacin da ake fama da annobar cutar Korona.

“Abin takaici ne yadda gwamnatin shugaba Buhari ta kasa daukar matakai na zahiri kan wannan batun mai tayar da hankali,” in ji kakakin PDP.

Jami’yyar PDP ta kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari wanda aka nada a matsayin jagoran yaki da cutar Korona a kasashen Ecowas ya gaza a cikin gida wajen shawokan matsalar da ake fama da ita a Kano.

Shugaba Muhammadu Buhari bai yi jawabi a hukumance ba game da wannan batun na mutuwar mutane da dama a Kano.

Sai dai hukumomi a jihar Kano a kwanakin bayan sun musanta alakar cutar covid 19 da mace-macen da ake yi a Kano.

Manyan jaridun Najeriya sun wallafa rahotannin da ke cewa a cikin kwana guda manyan mutane a Kano sun rasu cikin hadda manyan malaman jami’a da ‘yan kasuwa da manyan ma’aikatan gwamnati.

More from this stream

Recomended