Wata jihar Amurka ta maka China a kotu saboda coronavirus

AFP

Hakkin mallakar hoto
AFP

Missouri ta zama jihar farko a Amurka da ta maka gwamnatin China kara gaban kotu kan yadda ta tafiyar da annobar korona, wadda ta ce irin daukin da China ta kai ya janyo mata asarorin ta fuskar tattalin arziki.

Jihar Missouri dai tana karar gwamnatin China da Jam’iyyar Kwamunisanci mai mulki kan abin da ta kira tafka yaudara da gangan har ta janyo annobar kobid-19 a fadin duniya

“Gwamnatin China ta yi wa al’ummar duniya karya game da hatsari da kuma yanayin yaduwar annobar.

Haka zalika ta rika rufe bakunan masu kwarmata bayanai kuma ba ta yi wani kokarin a-zo-a-gani ba wajen hana cutar bazuwa,” in ji Atoni Janar na jihar Missouri Eric Schmitt.

Ya ce “Jazaman ne sai sun ba da bahasi kan matakan da suka dauka.”

Masu karar dai na neman a biya diyyar rayuka da wahalar da dan’adam da rikita harkokin tattalin arziki kamar yadda suka faru a cikin jihar.

China dai cikin kakkausar murya ta musanta yi wa batun rikon sakainar kashi.

Yayin da jami’an Missouri ke bayyana karar a matsayin wata aba “mai cike da tarihi”, masharhanta sun ce za ta iya fuskantar tarnakin shari’ah da na ka’idojin aikin hukuma don kuwa dokar Amurka ta bai wa gwamnatocin kasashen waje kariya daga irin wadannan matakai.

More from this stream

Recomended