
Mutanen jihar Borno sun jijjiga da jin labarin mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yaje musu a ranar Asabar.
Sakatare Janar na cigaban Bama, wato Bama Progressive Forum (BPF), Dr. Ali Bakari Mohammed, ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga mutanen baya.
A madadin mambobin kungiyar cigaban Bama da kuma mutanen karamar hukumar Bama da jihar Borno baki daya. Zamu cigaba da yi masa addu’a saboda irin aikin da yayi. Bayan haka shi mutum ne da zai zama abin koyi ga masu tasowa akan irin abubuwan da yake yi.
Barr. Zannah Mustapha, ya bayyana cewa ya samu labarin cikin tashin hankali, inda ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya dauki nauyin marayu 150 na tsawon shekara goma bayan sanadiyyar rikicin Boko Haram da ya ritsa da iyayensu.
Ya shafe shekaru 10 yana daukar nauyin marayu 150. Shugaban makarantar, daliban, da abokanan shi duka sun san da wannan abu da yake yi, kuma shi ya nemi kada mu bari wasu su san da maganar.” Cewar Barr. Hannah.
Sakataren wadanda suka samar da kungiyar cigaban Bama, Kachalla Grema Kyari, ya bayyana mutuwar shi a matsayin babban rashi mai cewo, musamman ma a yanzu da ake bukatar shi fiye da ko yaushe a Najeriya.