
—BBC Hausa
Bayan rasuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Najeriya Malam Abba Kyari, wasu masu sharhi kan harkokin siyasar kasar na ganin cewa yanzu hankali zai koma kan mutumin da zai gaje shi.
Marigayin ya rasu ne a jihar Legas ranar Juma’a bayan ya yi jinyar ‘yan makonni sakamakon cutar korona.
Kyari yana daya daga cikin makusanta Shugaba Muhammadu Buhari kuma yana cikin manyan masu karfin fada-a-ji a fadar shugaban kasar.
Hakan ya sa wasu ke ganin duk wanda ya maye gurbinsa, to akwai yiwuwar zai gaji kujerar ne tare da karfin ikon da marigayin ya rike a gwamnatin kasar.
Wani masanin harkokin siyasar kasar Dr Abubakar Kari na Jami’ar Abuja, ya ce zuwa yanzu akwai mutane da ake ganin wata kila daga cikinsu ne wani zai maye gurbin Malam Abba Kyari.
Dr Kari ya ce shi yana ganin “Ambasada Babagana Kingibe da Shugaban Hukumar Kwastam Kanal Hameed Ali da kuma Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu su ne ake kyautata zaton waninsu zai maye gurbin marigayin. ”
Ya ce Ambasada Kingibe, kamar marigayin shi ma ya fito ne daga jihar Borno kuma ya taba rike manyan mukaman gwamnati da dama a kasar.
Haka zalika ya ce mutum ne da ke da kusanci sosai da Shugaba Buhari a halin yanzu.
Har ila yau ya ce “Malam Adamu Adamu da Kanal Hameed Ali su ma makusantan Shugaba Buhari ne sosai kuma ba su da shamaki tsakaninsu da shi.”
“Don haka ba abin mamaki ba ne shugaban ya zabi guda daga cikin wadannan biyun,” in ji masanin siyasar.
Dokta Kari ya ce kujerar shugaban ma’aikatan shugaban kasa kujera ce mai muhimmanci sosai amma kuma da wuya a kwatantata da ta gwamna.
“Don haka sabanin yadda wasu mutane ke tunani, ni ba na jin Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna yana cikin jerin wadanda za a iya zaba su maye gurbin marigayi Abba Kyari,” in ji shi.
Ko da yake akwai wasu na ganin za a mika wa tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan AbdurRahman Dambazau kujerar ne saboda a cewarsu ya dade yana da muradinta.
Sai dai masanin siyasar ya ce ganin yadda Shubaba Buhari bai dawo da tsohon ministan mukaminsa ba a karo na biyu, “to wata kila da wuya shi ma ya samu wannan kujera.”
Babban jami’in walwala na kasa a jam’iyya mai mulkin kasar wato APC, Alhaji Ibrahim Masari, ya ce kada a yi riga malaman masallaci kan wannan batu.
“Tun da wannan ba mukami ba ne na zabe, to kamata ya yi mu yi hakuri, mu jira shugaban kasa ya fita daga yanayin juyayin wannan rashi.”
“Sannan daga bisani ya bayyana wanda yake ganin shi ya fi dacewa ya maye gurbinsa,” in ji shi.
Hammeed Ali
Shi ne shugaban hukumar kwastam na Najeriya. Ya kasance da Shugaba Buhari na tsawon lokaci tun suna soja. Ana kallonsa a matsayin wanda Buhari ya amince da shi wajen rikon amana.
Wani abu da Hameed Ali yake da shi a cewar makusantarsa shi ne baya son ana cin hanci kuma yana da taka tsantsan a al’amuransa.
Idan ya samu kujerar, watakila ‘yan siyasa za su ci gaba da guna-guni saboda kasancewarsa yana aiki ba-sani ba sabo.
Adamu Adamu
Hakkin mallakar hoto
Adamu Adamu Twitter
Shi ne ministan ilimi tun daga farkon mulkin Shugaba buhari a shekara ta 2015. Ya yi aiki tare da Buhari tsawon lokaci kuma yana daga cikin wadanda ba a yi musu iso wajen shiga Fadar Aso Rock.
Malam Adamu ya kasance marubuci na tsawon shekaru kuma yana tsokaci sosai kan al’amuran da suka shafi yau da kullum a Najeriya.
Nada shi kamar wani na cikin gida ne ya kara samu kuma ‘yan siyasa na waje za su iya cewa bata sauya zani ba.
Nasir Elrufai
Gwamnan jihar Kaduna wanda kuma a yanzu haka shi ma yana jinyar cutar korona wacce ta kashe Malam Abba Kyari.
Bayanai sun nuna cewa ya yi kamun kafa wajen neman wannan kujerar a bara, sai dai babu wata hujja da BBC ta samu da ta nuna hakan.
Tun daga lokacin da Buhari ya kafa jam’iyyar CPC, El Rufai yake abokin tafiyar shugaban kasa kuma yana cikin wadanda ake kallo a masu fada a ji a wannan gwamnatin.
Hakkin mallakar hoto
Kaduna Govt
Idan ya samu kujerar kamar yadda masu sharhi suke cewa, to tamkar wata dama ce gare shi ya tabbatar da aniyarsa ta zama shugaban kasa a shekarar 2023 idan Buhari ya kammala wa’adinsa.
Sai dai wasu na ganin ya cika janyo ce-ce-ku-ce abin da watakila zai iya shafarsa.
Babagana Kingibe
Tun bayan da Shugaba Buhari ya dawo mulki a karo na biyu, Kingibe ya soma dasawa da gwamnatin kasancewarsa na jiha daya da marigayi Malam Abba Kyari.
Sai dai tsarin siyasarsa a baya za ta iya shafar burinsa a yanzu, saboda lokacin da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Yaradua yake kan mulki ya cire Kingibe a matsayin sakataren gwamnatin tarraya bayan ya dawo daga jinya.
Sannan yadda ta kaya bayan an sake zaben MKO Abiola a shekarar 1993, inda Kingibe wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa, sai kawai ya koma cikin gwamnatin soji ta su Janar Sani Abacha aka ba shi mukamin minista, ya sa wasu ke dari-dari da shi musamman mutanen kudu maso yammacin Najeriya.
Ana ganin yana da gogewar aikin gwamnati amma kuma wasu ‘yan siyasa na kuka da salon tsarinsa.