
Hakkin mallakar hoto
Kano State
Gwamna Ganduje ya dauki matakin hana zirga-zirga a jihar
Shugaban kwamitin da ke yaki da cutar korona a Kano ya kamu da cutar kamar yadda wata majiya mai karfi ta tabbatarwa da BBC.
Sai dai kawo yanzu gwamnatin jihar Kano bata tabbatar da wannan lamarin ba a hukumance.
Sannan kuma majiyar ta ce baya ga shugaban kwamitin, wasu mutum biyu ma mambobin kwamitin sun kamu da cutar, kuma tuni su ukun suka killace kansu.
Kano dai a yanzu ita ce ta uku wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya, baya ga Legas da Abuja, kuma har ma ta yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Laraba.
A yanzu dai mutum 21 ne ke dauke da cutar a jihar kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta sanar a shafinta na Twitter.
A hirarsa da BBC kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al’ummar jihar.
Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa ‘A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya’, ko da yake daga bisani an amince a rka daukar mutum biyu.
Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.
Kazalika, a ranar da maraice dokar hana shiga da fita ta fara aiki a jihar, inda zuwa Juma’a da safe birnin ya zama fayau kowa yana cikin gida.
Sannan malaman jihar ma sun amince da matakin dakatar da Sallar Juma’a don hana yaduwar cutar.
Mutane sun yi ta rububin sayen kayan abinci a ranar Alhamis inda kasuwanni suka cika makil.
Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.