Wautar wasu tsiraru na iya janyo halakar jama’a – Buhari | BBC Hausa

@BashirAhmaad

Hakkin mallakar hoto
@BashirAhmaad

Image caption

Shugaba Buhari ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da aiki da umarnin

Shugaba Buhari ya ce zuwa yanzu sun gano kashi 92% na mutanen da suka yi hulda da masu fama da korona, tare da ninka yawan dakunan gwaje-gwaje a Najeriya.

Ya kuma bayyana fatan kara yawan gwajin masu cutar korona zuwa mutum 1,500 kullum a fadin kasar.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar da maryacen ranar Litinin inda ya sanar da tsawaita matakin kulle jihohin Legas da Ogun da kuma Babban Birnin Tarayya.

Shugaban ya ce sun horas da ma’aikatan lafiya sama da 7,000 kan riga-kafi da matakan dakile cutuka masu yaduwa, yayin da hukumar NCDC ta aika jami’anta zuwa jiha 19 a kasar.

Jawabin na zuwa ne daidia lokacin masu cutar korona suka karu zuwa sama da mutum 340 a fadin Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A cewarsa: “Lagos da Abuja a yau suna da karfin karbar marasa lafiya dubu guda a fadin cibiyoyin kwantar da masu cutar korona da ke fadin biranen biyu”.

Ya kuma ce ta hanyar amfani da dukiyar kasar da kuma gudunmawar da suka samu, za su wadata cibiyoyin ciki har da na jihohi da ma’aikata da kayan aiki a ‘yan makwanni masu zuwa.

Buhari ya ce tuni suka samar wa ma’aikatan lafiya a dukkanin cibiyoyin kula da masu korona rigunan kare lafiya don su sanya, su gudanar da ayyukansu cikin aminci.

“Fata da addu’o’inmu su ne ba sai mun yi amfani da wadannan cibiyoyi ba, amma dai duk da haka za mu shirya don gudun abin da ka je ya zo” in ji shi.

Ya ce a matsayinsu na zababbun shugabanni sun tsaida wannan shawara ce mai wahalar gaske duk da yake sun sani za ta hargitsa harkokin rayuwa kuma ta sanya ‘yan kasa da ababen kaunarsu da al’ummominsu cikin takura.

Hakkin mallakar hoto
@MBuhari

Sai dai a cewar shugaban wannan sadaukarwa ce ake bukata don takaita bazuwar cutar kobid-19 a kasar. “Sun zama dole don kubutar da rayuka”.

Buhari ya ce: “manufarmu har yanzu ita ce shawo kan bazuwar korona da kuma samar da sarari, lokaci da kayan aiki don daukar gagarumin mataki na bai daya.

Ya ce sakamakon gagarumin goyon baya da hadin kan da suka samu, sun cim ma dumbin nasarori a cikin kwana 14 da aka kulle biranen tun da farko.

A cewarsa, kasar ta hau kan hanya don samun nasara a yaki da annobar.

Sai dai ya ce duk da haka har yanzu yana cike damuwa kan karuwar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka rasu a fadin duniya da ma musamman a Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yadda babbar hanyar Ikorodu ta Legas ta zama wayam sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar.

“A ranar 30 ga watan Maris 2020, lokacin da muka daukar matakin kullewar kamar yadda likitoci da masana kimiyya suka ba da shawara, jimillar masu cutar a fadin duniya sun dan haura 780,000.

To amma jiya, adadin masu cutar a fadin duniya ya zarce 1,850,000. Wannan adadi ya fi karfin ninki biyu.”

Ya ce a cikin kwana 14 kawai, fiye da mutum 70,000 cutar korona ta yi ajali. Kuma a dai wannan lokaci, mun ga yadda kwayar cutar sha kan harkokin kula da lafiya hatta a kasashe mafi karfin arziki.

Muhammadu Buhari ya ce a Najeriya, akwai mutanen da suka kamu da cutar korona 131 a jiha 12 ranar 30 ga watan Maris, mutum biyu kuma sun riga mu gidan gaskiya.

“Da safiyar nan Najeriya tana da mutum 323 da ke da cutar a cikin jiha 20. Abin takaici kuma a yanzu muna da mutum da suka rasu,” in ji shugaban.

Ya ce jihar Legas na da kashi 54% na mutanen da aka tabbatar sun kamu da korona a Najeriya. Idan aka hada da na Abuja, wuraren biyu na da sama da kashi 71% na wadanda suka kamu.

Don haka: “Mafi yawan kokarinmu zai fi karkata zuwa wadannan wurare guda biyu”.

Shugaba Buhari ya ce Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta sanar da shi cewa gagarumin adadi na mutane sabbin kamuwa da ake samu a yanzu na faruwa ne a tsakanin ‘yan kasa, ta hanyar hulda tsakanin mutum da mutum.

Saboda haka ya tunasar da dukkan ‘yan Najeriya su ci gaba da daukar alhaki na matakan da ake ba da shawarwari ta kare yaduwar cutar ciki har da yin nesa-nesa da juna da tabbatar da tsabtar jiki, sannan kuma a zauna a gida.

Bugu da kari ya ce ya sanya hannu kan dokar killace mutane tare da bijiro da karin ka’idoji don fayyace matakan shawo kan annobar korona, kuma nan gaba kadan za a fitar da su.

Buhari ya ce ba abin raha ba ne. Magana ce ta tsakanin rayuwa da mutuwa. An rufe Masallatan Harami a biranen Makkah da Madina. Fafaroma ya yi bikin ranar Ista a Dandalin St Peter fayau ba tare da mahalarta ba.

Haka kuma an yi bikin na Ista a mashahuriyar majami’ar Notre Dame ta birnin Paris da mutanen da suka gaza goma. Kasashen Indiya, da Italiya da Faransa duk an kulle su. Sauran kasashe ma suna kokarin bin sahu. “Ba za mu sake ba” in ji shi.

Ya ce mako biyu da ya wuce, gwamnati ta sanar da matakan rage radadi da suka hadar da rabon kayan abinci da tallafin kudi da jinkirta karbar basuka don sassauta tsananin da matakansu za su janyo a irin wannan mawuyacin lokaci.

Shugaban ya ce ya kuma ba da umarnin cewa a fadada rijistar tallafa wa masu karamin karfi daga gida miliyan biyu da 600,000 zuwa gida miliyan uku da 600,000 a cikin mako biyu mai zuwa.

Ya kuma nanata kira ga ‘yan Najeriya su bi umarnin zama nesa-nesa da juna. A cewarsa “rashin hankalin wasu ‘yan kalilan na iya janyo mutuwar mutane da dama. ‘Yancin mutum na karewa ne inda hakkin mutane ya fara.

Image caption

Wasu mazauna unguwar Karu kenan da ke Abuja yayin da wasu mazauna unguwar ke kokarin fita duk da dokar da aka sa.

Muhammadu Buhari ya kuma ce don tabbatar da ganin tattalin arzikin kasar ya dace da sabbin al’amuran da ke faruwa. “Ina umartar ma’aikatar masana’antu, ciniki da zuba jari da takwararta ta sadarwa da bunkasa tattalin arzikin dijital da ma’aikatar kimiyya da fasaha da ta sufuri.

Gami da ma’aikatar sufurin jiragen sama da ta harkokin cikin gida da ma’aikatar ayyuka da gidaje da ta kwadago da samar da aikin yi da ma’aikatar ilmi su hada gwiwa don bullo da wata bakandamiyar manufa ta yadda tattalin arzikin Najeriya zai iya aiki duk da annobar korona.”

Buhari ya kuma uamarci ma’aikatar noma da raya karkara da mashawarcinsa na musamman kan harkokin tsaro da shugaban majalisar bunkasa ayyukan wadata kasa da abinci da shugaban shirin samar da takin zamani na shugaban kasa su yi aiki da kwamitin yaki da korona don rage tasirin wannan annoba kan al’amuran noma a damunar bana.

More from this stream

Recomended