
Hakkin mallakar hoto
Nigerian Government
Gwamnati ta ce za ta samar da kudin ne domin inganta bangaren lafiya a ci gaba da yaki da coronavirus
Gwamnatin Najeriya na shirin kirkirar wata gidauniya ta kudi naira biliyan 500 domin inganta sashen lafiya a kasar a yakin da take yi da annobar cutar coronavirus, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Asabar.
Ministar Kudi Zainab Ahmed ta gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da takwaransa na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, inda suka amince cewa za a tattaro kudin ne daga asusun ma’aikatu daban-daban na kasar.
Kazalika za a ciyo bashin wasu kudin daga cibiyoyin bayar da bashi na kasashen duniya, kamar yadda suka bayyana a wani bayani wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
“Wannan kudi za a yi amfani da su ne domin habaka cibiyoyin lafiya,” in ji Ahmed Lawan.
Kudirin na gwamnati na bukatar amincewar majalisar tarayya kafin a iya aiwatar da shi, wadda kuma a yanzu take cikin hutu na mako biyu.
Sai dai Ahmed Lawan ya ce za su yi bakin kokarinsu wurin amincewa da kudirin.
Ya ce: “Idan ana bukatar mu dawo bakin aiki domin taimakawa wurin ganin gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan abubuwan ci gaba za mu yi hakan.”
Ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin, Najeriya na da masu cutar coronavirus 224, mutum biyar sun mutu sannan 27 sun warke.
Cibiyar bayar da lamuni ta duniya wato IMF ta tanadi dala biliyan 50 na gaggawa da za ta bai wa kasashe rance.
Tuni kasashe kusan 80 suka nemi tallafin, 20 daga cikinsu daga Nahiyar Afirka, a cewar Reuters.
A makon da ya gabata ma sai da babban bankin Najeriya CBN ya kaddamar da wani yunkuri na samar da naira biliyan 120 daga kamfanoni masu zaman kansu domin agaza wa bangaren lafiya ta yadda za a yaki annobar coronavirus.