
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
—BBC Hausa
Ana saran kusan mutum miliyan biyu za su yi Aikin Hajji bana
A ranar Laraba 1 ga watan Afrilun 2020, Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden maniyyata aikin Hajjin bana, a yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da mamaye duniya.
Ministan Aikin Hajji Mohammed Banten wanda ya ba da sanarwar, ya ce Saudiyya ta damu da tsaron lafiyar Mahajjata sannan ya yi kira ga jama’a su “jira kafin su biya kudin” aikin Hajji.
Ana sa ran fiye da Mahajjata miliyan biyu ne za su tafi Kasa mai tsarki a watan Yuli zuwa Agusta domin gudanar da aikin Hajji, amma ganin yadda coronavirus ke ci gaba da yaduwa a Saudiyya, da ma duniya baki daya, ya sa ana tababa anya hakan mai yiwuwa ne?
Dole ne dukkan Musulmin da ke da lafiya da halin zuwa ya yi aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsa.
Amma wannan sanarwa ta sa tuni hankulan wasu Musulman ya tashi kan tsoron a wayi gari a ce babu aikin Hajji a bana.
A makon da ya gabata ne cibiyar bincike da adana bayanai ta Sarki Abdulaziz wato (King Abdulaziz Foundation for Research and Archives) ta fitar da wata sanarwa da ke bayani kan lokuta 40 a tarihi da ba a yi aikin Hajji ba ko kuma aka samu karancin alhazai.
BBC ta yi bincike tare da duba kan lokutan da ba a yi aikin Hajji ba a duniya tun kafuwar Musulunci ta bakin wasu malamai a Najeriya.
Za a iya cewa tun lokacin da wannan sabuwar Daular Saudiyya karo na uku ta kafu ba a taba samun shekarar da ba a yi aikin Hajji ba, shi ya sa mutane da dama ke ganin kwata-kwata a duniya babu shekarar ma da ba a yi aikin Hajji ba.
”Yawanci idan ba wadanda suka karanci tarihi ba, ba lallai su san da hakan ba,” in ji wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, wanda kuma ya karanci Fannin Hadisi a Jami’ar Madina, wato Dr Ibrahim Disina.
Amma an sha soke aikin Hajji a lokuta da dama a tarihin Musulunci saboda ko dai yake-yake ko annoba ko masu kai hari.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Shekara ta 317-327 bayan Hijira
An shafe shekara 10 daga shekara ta 317 zuwa ta 327 bayan Hijira ba a yi aikin Hajji ba.
A shekarar farko ta 317 din ne aka samu wani dan tawaye Abu Taher al-Janabi al-Qurmuty jagoran Daular Qaramida wanda ya afka wa alhazai a shekara ta 316.
Ya karkashe kusan mutum 30,000 ya zuba gawarwakinsu a Rijiyar Zamzam kuma ya ragargaza rijiyar, ya dauke Hajrul Aswad ya tafi da shi garinsu na Hijr, wanda a yau shi ne Qatif da ke gabashin Saudiyya.
”Saboda tsoron wannan dan ta’adda ne ya sa alhazai suka shafe shekara 10 ba su je aikin Hajji ba har sai da Allah ya kawo saukin lamarin, kamar yadda Imamul Zahabi ya fada a cikin littafinsa na Tarikhul Islam,” a cewar Dr Disina.
Shekara ta 357 bayan Hijira
Ibn Kathir a littafinsa Albidaya Wannihaya ya ambaci labarin wata annoba da aka yi mai suna annobar Almashidi wadda ta kashe alhazai tun a kan hanya.
”Kashi uku cikin hudu na alhazai duk sun mutu, ragowar kashi dayan ma annobar ta ci gaba da uzzura musu har cikin garin Makkah, abin da ya hana gudanar da aIkin Hajji a wannan shekara,” in ji Disina.
Latsa hoton da ke kasa don sauraron cikakken bayani daga bakin Malamin:
Na’urarku na da matsalar sauraren sauti
Shekara ta 492 bayan Hijira
A wannan shekara ma, ba a samu damar yin aikin Hajji ba saboda sabani da aka samu tsakanin sarakunan wancan lokaci dalilin rashin wata daula guda daya da ke jagorantar daukacin Musulman duniya.
Dr Disina ya ce ”Hakan ya sa aka yi ta samun rikici tsakanin sarakuna musamman idan an je aikin Hajji don haka mutane suka kaurace wa aIkin Hajji ma a wancan lokacin.”
Shekara ta 654-658 bayan Hijira
A wadannan shekaru guda hudu ma a jere ba a yi aikin Hajji ba, sai ‘yan cikin garin Makkah ne kawai saboda rikita-rikitar da aka yi ta samu
Shekara ta 390 bayan Hijira
Akwai shekarun da ba a samu wasu yankuna na duniya ba su je aikin Hajji ba, kamar shekarar 390 bayan Hijira zamanin Sarki Azeez Billahil Fadimi inda mutanen kasar Masar baki daya ba wanda ya samu zuwa aikin Hajji saboda tsadar rayuwa.
”Kuma a lokacin Masar kasa ce mai girma da ta fi yadda take a yau.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Shekara 40 da ta wuce wani malami mai kwarjini da mabiyansa suka kwace iko da Masallacin Ka’aba da bakin bindiga
Shekara ta 419 bayan Hijira
A wannan shekara ma mutanen Mashriq wato kasashen arewacin Afirka kenan da Spaniya inda Daular Musulunci take a da, su ma ba su je aikin Hajji ba saboda rikita-rikitar da aka samu a tarihi.
Shekara ta 421 bayan Hijira
Ita ma Dr Disina ya ce tarihi ya nuna mafi yawan mutanen duniya ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba.
Shekara ta 1231 bayan Hijira
Malam ya ce ko a nan baya-baya, an samu shekarun da ba a yi Hajji ba, lokacin da ‘yan mulkin mallaka ke kokarin mamayar kasashen Musulmai, duk da cewa Allah yakan kare biranen Makkah da Madina daga masu kokarin mamaya.
”A wancan lokacin kokarin mamayar ya sa alhazai suka ji tsoron zuwa iikin Hajji,” in ji shi.