
An sake samun karin sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar Covid-19 a Najeriya ciki harda birnin tarayya Abuja.
Ministan lafiya,Osagie Ehanire shi ne ya sanar da haka ranar Asabar.
Ya ce an samu wadanda suka kamu da cutar a birnin tarayya Abuja da kuma jihohin, Ekiti,Ogun,Lagos.
Hakan na nufin cewa an samu jumullar mutane 22 da suka kamu da cutar a Najeriya.
Dukkanin mutane ukun biyu maza da kuma mace daya da aka samu suna dauke da cutar a Abuja sun dawo ne daga kasashen waje tsakanin ranakun 14 zuwa 18 ga wata.