
Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau
—BBC Hausa
Gwamnatin Najeriya ta ce ta gamsu da irin matakan da take dauka domin dakile bazuwar cutar coronavirus a kasar.
Najeriya na cikin kasashen Afirka 26 da cutar coronavirus ta bulla, kuma wasu kasashen sun dauki matakai na haramta taron jama’a da rufe iyakoki da dakatar da zirga-zirga daga kasashen da cutar ta fi shafa domin dakile bazuwarta a kasashensu.
Mutum biyu aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya, kuma gwamnatin kasar ta ce zuwa yanzu ba za ta haramta zirga-zirga kan wata kasa ko sufurin jiragen sama ba saboda tsoron bazuwar coronavirus.
Ma’aikatar lafiya a kasar ta ce sun dai dauki karin matakai don kare bazuwar cutar, tare da karfafa hanyoyin bin sawun mutanen da suka yi hulda da masu dauke da cutar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Buhari ta gamsu da irin matakan da aka dauka don dakile bazuwar cutar a kasar.
Ya ce ana gwaji a filayen jiragen sama da ake shigowa daga kasashen waje, kuma a yanzu gwamnati ba ta bukatar daukar matakan hana zirga-zirgar jiragen da ke fitowa daga kasashen da cutar ta fi shafa.
“Babu bukatar a dauki irin wadannan matakan a yanzu.”
“Gwamnatin tarayya ta yi tanadin kudi naira biliyan guda da aka ba ma’aikatar lafiya domin sayen kayan aiki na gwaje-gwaje a filayen jiragen sama.
“Kuma an yi gargadi ga jami’an gwamnati idan tafiya ba dole ba ce a daina,” inji Garba Shehu.
Ya kuma ce akwai kwamiti da gwamnati ta kafa gwamnani karkashin jagorancin sakataren gwamnati domin bunkasa matakan da ake dauka.
Ya ce babu ribar zuzuta abu, domin daukar wasu matakai na iya rikita al’ummar kasa game da cutar.