
Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da mambobinta su biyar kan zargin da ake musu na yunkurin sace sandar majalisar.
A ranar Litinin da ta gabata ne wasu daga cikin mambobin majalisar suka hana zaman majalisar bayan da kwamitin da majalisar ta kafa ya binciki tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sunusi yayi shirin mika rahotonsa.
An ce yan majalisar sun nuna kin amincewarsu da mika rahoton kwamitin kan gaza cikar wa’adin mako guda da tun farko aka bawa kwamitin.
Mambobin da abin ya shafa sun fito ne daga jam’iyun APC da PDP kuma an dakatar da su na tsawon watanni shida.
Abdulaziz Garba Gafasa, shugaban majalisar wanda ya sanar da dakatarwar a yayin zaman majalisar na ranar Litinin ya ce yan majalisar sun yi abinda ya sabawa dokokinta.
Mambobin da aka dakatar sun hada da:
- Garba Yau Gwarmai (APC)
- Labaran Abdul Madari(APC)
- Isyaku Ali Danja(PDP)
- Muhammad Bello (APC)
- Salisu Maje Ahmad Gwangwazo