Kwankwaso Ne Ya Fara Zubar Da Darajar Masarautar Kano – Ra’ayin Sani Bn Aliyu – AREWA News

Na sha fada a baya yanzu ma zan kara maimaitawa cewa, tun da Rabi’u Fulamba Kwankwaso ya zubar da darajar masarautar Kano ba ni da bukatar komai a wajen ta, saboda shi gidan Dabo ba gida ne na siyasa ba.

Amma don bakar kiyaiyyar da Kwankwaso yake yi ga marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Ado Abdullahi Bayero, na tattara sarauta na ajiye.

Ko shakka babu wajibi ne a gare ni na godewa Allah da ya sa na ga karshen zaman Sunusi a kan kujerar Dabo.

Allah ya taimaki Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Adamu Abdullahi Bayero, wanda dama shi ya cancanta.

Na tabbata Mai Martaba Sarki ba zai ci amanar jama’a ba don kuwa shi dan amana ne irin mahaifin sa marigayi Adamu Abdullahi Bayero.

Shi kuwa Sunusi ya je can idan yaso ya dawo neman kujerar gwamna kamar yadda ‘yan Kwankwasiyya suke fada.

Allah ya taimaki Sardaunan Kano Aminu Ado Bayero, don kaunar da muke yi wa Annabi Muhammadu SAW.

More from this stream

Recomended