Ministar Lafiyar Birtaniya ta kamu da cutar Coronavirus | BBC Hausa

Ministar Lafiyar Birtaniya, Nadine Dorries ta kamu da cutar Coronavirus, ita ce ‘yar majalisar dokokin kasar ta farko da ta kamu da cutar.

Ministar ta sanar cewa a yanzu ta killace kanta a gida, yayin da hukumomi ke ta kokarin gano inda ta kwaso cutar.

Ko a ranar Alhamis ta halarci wani taron cin abinci da Fira minista Boris Johnson ya shirya a fadar gwamnati da ke titin Downing.

Kusan mutun 400 ne cutar coronavirus ta kama a Birtaniya inda shida suka mutu.

Misis Dorries ta ce ta damu matuka kan makomar lafiyar mahaifiyarta mai shekara tamanin da hudu wadda a yanzu haka suke zaune a gida daya.

More from this stream

Recomended