Jamiyyar PDP tace bakomai bane ya kawo bullar Corona virus a Najeriya ba face sakaci da kuma rashin kulawa da shugaban kasa Buhari yake nunawa wajen barin mutanan da cutar ta billa a kasar su suna shigowa kasarmu ba tare da bincike ba.
Jamiyyar tace wannan ma babbar alamace ta gazawar gwabnatin Buhari wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa , inda ta kasa daukar mataki domin hana wannan cutar shigowa Najeriya.
Jamiyyar tace duk gwabnatin da take da kishi kuma ta damu da al’ummar ta to dole ta samar da kyakkyawar kulawa a dukkan mashigar kasar ta amma mu da yake mun hadu da gwabnatin da bata damu da al’ummar ta ba mu abun da tafi damuwa dashi shine yada k’arya da cogen aiki da kuma kurin tana kokari .
PDP tana kiran yan Najeriya dasu tashi tsaye wajen kiran kungiyoyi , masu bada agaji su zo su bada gudunnawa don ganin wannan jinyar bata yadu ba , musamman duba da halin rashin tsaro , matsalar tattalin arziki da ya dabai baye kasar nan.
Jamiyyar tace tana kiran gwabnati data gaggauta daukar mataki kamar yadda PDP tayi a 2014 lokacin da Ebola ta shigo Najeriya.
PDP tana bawa yan Najeriya shawara dasu kula da dukkan sharudan da aka fada musu don ganin cutar nan bata yadu ba .
Jamiyyar tana kiran ma’aikatar lafiya da tayi dukkan abun da zatayi don kawo karshen wannan cutar kuma kada ta bari labaran k’arya su shiga cikin wannan abun.