
Joe Biden
Mista Biden ya lashe Texas da North Carolina da Massachusetts da Minnesota da Oklahoma da Arkansas da Alabama da Tennessee da kuma Virginia.
Sai dai ana ganin cewar Bernie Sanders ne ya lashe California – wadda ita ce jihar da ta fi yawan kuri’u – da kuma wasu jihohi uku.
Mista Biden da Mista Sanders dai na gwabzawa ne a zaben fitar da gwani domin tunkarar Donald Trump na jam’iyyar Republican.
Tsohon Magajin Garin New York Michael Bloomberg ya kashe sama da dala miliyan 500 daga aljihunsa yayin yakin neman zabe, sai dai ko jiha daya bai samu nasarar ci ba.
Wakilan jam’iyya sama da 1300 ne cikin 1,991 suka jefa kuri’a a Babbar ranar Talata da ake kira Super Tuesday inda su ne za su fitar da wanda zai tsayawa jam’iyyar Democrats takara a babban zaben kasar.
A halin yanzu dai Mista Biden na da kuri’a 396, yayin da Mista Sanders yake da kuri’a 314.