Martanin wasu ‘yan Najeriya game da bullar Coronavirus a kasar

.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

_BBC Hausa

Tun bayan da hukumomi a Najeriya suka tabbatar da bullar cutar coronavirus da ake kira Covid-19 a jihar Legas, dubban ‘yan kasar ke ci gaba da tafka muhawara a shafukan sada zumunta musamman Twitter da Facebook.

Tun a ranar Laraba aka fara yada jita-jitar labarin bullar cutar a jihar Legas a shafukan intanet bayan kwantar da wani dan China a asibitin Reddington da ke Ikeja.

Wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos kamar yadda ministan lafiya na Najeriya Dakta Osagie Ehanire ya tabbatar.

Sai dai wasu a shafukan sada zumuntar, suna ganin ”sakaci” ne daga hukumomin kasar yasa har cutar ta samu bulla.

Wasu kuma na ganin bular cutar coronavirus, tamkar kara wa Borno dawaki ne ga matsalolin da ake fama da su a Najeriya.

Mau’du’an da ake amfani da su wajen tafka muhawara a shafin Twitter kan bullar cutar a Najeriya sun hada da #COVID19Nigeria da kuma #coronavirusinlagos.

Bayan bullar wannan cuta, BBC ta ziyarci asibitin da aka ware na musamman domin magance yaduwar cutar COVID-19 kuma asibitin yana a birnin Legas.

Wasu kuma yayin muhawarar, addu’a suke yi domin Allah ya kawo sauki dangane da wannan lamari.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

â–  Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina – sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

â–  Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

â–  Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi – za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. – akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Alamomin cutar coronavirus

Wadanne ne alamomin cutar?

Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.

Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.

Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.

More from this stream

Recomended