Real Madrid na iya sayo Mohamed Salah, Mourinho zai fafata da Man Utd a kan Forsb

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Madrid ta yi amannar cewa za su iya sayo Mohamed Salah idan suka rabu da Gareth Bale

Kocin Tottenham Jose Mourinho na fatan fafatawa da tsohon kulob dinsa Manchester United wajen zawarcin dan wasan RB Leipzig mai shekara 28 dan kasar Sweden, Emil Forsberg. (Express)

Inter Milan sun tuntubi Tottenham kan ko za su samu dan wasan Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 32, wanda har yanzu bai amince da sabon kwantaragi ba (Standard)

Real Madrid ta yi amannar cewa za su iya sayo dan wasan Liverpool dan kasar Masar Mohamed Salah, mai shekara 27, a kan £126m bayan sun rabu da dan kasar Wales Gareth Bale, mai shekara 30. (El Desmarque, via Express)

Manchester United na shirin sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 27, da takwaransa dan Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24, domin samun kudin sayo dan wasan Aston Villa Jack Grealish, 24. (Express)

Arsenal ta yi yunkurin sabunta tattaunawar da take yi da dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, a yayin da kwantaragin da ake biyansa £200,000 duk mako zai kare a karshen kakar wasan da muke ciki. (Times, subscription required)

Bayern Munich na tuntubar wakilan dan wasan Liverpool dan kasar Brazil Roberto Firmino, mai shekara 28. (Echo)

Kazalika, tattaunawar da Liverpool ke yi da RB Leipzig kan Timo Werner, mai shekara 23, ta yi nisa. (Express)

  • Man City ta yaga barakar Real Madrid a Spaniya
  • Kotun Koli ta yi watsi da karar APC kan zaben Bayelsa

Kocin Inter Antonio Conte yana son sayo daya daga cikin ‘yan wasan bayan Chelsea, inda yake duba yiwuwar dauko ko dai dan wasan Spain Marcos Alonso, mai shekara 29, ko takwaransa dan Italiya Emerson Palmieri, mai shekara 25, a bazara. (Tuttosport, via Mail)

Dan wasanChelsea dan kasar Brazil Willian, mai shekara 31, ya ce kwantaragin da kungiyar ta yimasa tayin sanyawa hannu bata gamsar da shi ba inda ya ce yana “tsaka mai wuya”. (Esporte Interativo, via Football 365)

Roma na son sayo dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, da takwaransa dan Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31, a yarjejeniya ta din-din-din. Smalling yana Manchester United, yayin da Mkhitaryan yake Arsenala matsayin aro. (Sky Sports)

Arsenal, Newcastleda Southampton na sanya ido kan Hoffenheim da kuma dan kasar Austria Florian Grillitsch, mai shekara 24. (Sport Bild, via Chronicle)

Dan wasanBarcelona dan kasar Spain Sergio Busquets, mai shekara 31, ya soki yadda kungiyar ke musayar ‘yan kwallo saboda rashin tsari. (ESPN)

Real Madrid na shirin biyan euro 70m domin sayo dan wasan Napolimai shekara 23 Fabian Ruiz. (Calciomercato – in Italian)

More from this stream

Recomended