
Dalibai likitoci masu koyon sanin makamar aiki a Faransa na zanga-zanga saboda rashin kayan aiki da sauran abubuwan da suke bukata
Magadan gari tara a Faransa sun haramta rashin lafiya a wani mataki na nuna rashin likitoci a garuruwansa.
Kudurin dokar wadda magadan garin suka sanya wa hannu a wasu yankuna da ke Sarthe a yammacin birnin Paris, ya ce an haramta kiran likita saboda wata rashin lafiya ko kuma hatsarin mota.
Sun ce manufarsu ita ce su gargadin gwamnatin kasar a kan wahalhalun da ake fama da su wajen samun likitoci a yankunansu.
Matsalar ma’aikatan lafiya da karancin gadajen kwanciya a asibitoci da kuma rufe wuraren kula da lafiya na daga cikin matsalolin da suka ambata.
A cikin dokar, an hana ganin likita ko da kuwa hatsarin mota ne ko kuma haihuwa a yankunan.
To sai dai kuma a cikin dokar, an amince mutum ya tafi Paris ya je neman magani.
Ya ce “Wannan matsala ta shafe mu, ta kuma shafi al’ummarmu, don haka dole ne gwamnati ta yi wani abu akai”.
Mista Dhumeaux, ya ce ” Mutane dubu 70 daga cikin dubu 560 da ke zaune a yankunanmu ba sa samun damar ganin likita”.
Ya ce saboda yanayin kauyukan da kuma rashin asibitoci da ma likitoci na sanya rayuwar marasa lafiya cikin babban hadari.
Samun damar kula da lafiya ta zamo babbar abar damuwa a kasar Faransa.
A shekarar 2019, wani bincike ya gano cewa, fiye da mutane hudu daga cikin goma ‘yan kasar Faransa, sun hakura da zuwa asibiti neman magani saboda dogon jira.

