‘Yan matan bogi na Hamas sun yi kutse a wayoyin sojojin Isra’ila | BBC Hausa

Image purportedly used in Hamas honey trap

Hakkin mallakar hoto
IDF

Image caption

Daya daga cikin hotunan da ake zargin kungiyar Hamas ta yi amfani da su a lokacin kutse

Gwamman sojojin Isara’ila sun fada tarkon mayakan Hamas inda mayakan suka yi kutse a wayoyin salular sojojin ta hanyar fakewa a matsayin mata suna tura musu sakonni.

Rundunar sojin Isra’ila, ta bayyana cewa mayakan sun ta turo hotunan ‘yan mata ta wayoyin sojojin inda suke jan hankalinsu domin sauke wata manhaja a wayoyinsu, ba tare da sanin cewa manhajar ba ce za ta bayar da damar yin kutse a wayoyinsu.

Mai magana da yawun rundunar sojin ya shaida cewa mayakan ba su samu wasu muhimman bayanai daga wayoyin ba har zuwa lokacin da aka gano su.

Kungiyar Hamas wadda ke da iko da Gaza ta dade tana ‘yar tsama da Isra’ila.

Wannan ne karo na uku a cikin shekarun nan da Hamas din ke kokarin yin kutse ga wayoyin sojojin Isra’ila kuma kutsen da suka yi a wannan karon ya fi rudani, in ji Laftanar Kanal Jonathan Conricus.

”Mun ga alama suna kara jajircewa wajen wannan wasan nasu,” in ji shi.

Kanal Conricus ya ce masu kutsen sun yi shigar burtu a matsayin ‘yan mata ‘yan ci rani inda suke amfani da yaren Hebrew wanda da sojojin sun karanta rubutunsu, sai su dauka kamar baki ne da ba su goge sosai a yaren ba.

Bayan sun amince da matan kuma abota ta yi nisa, matan sukan aika wa sojojin hotunansu, wanda da zarar sun sauke hotunan a wayoyinsu, sai su samu damar yin kutse a wayoyin sojojin.

Idan suka yi kutse a wayoyin, za su samu damar daukar hotuna da kuma sautin murya ba tare da masu wayoyin sun sani ba.

Isra’ila da Hamas na cikin wani rikici wanda ya ki ci ya ki cinyewa kuma duka suna kokarin tattara bayanan sirri tsakanin junansu.

Related Articles