Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ce kimanin mutum 22 ne suka mutu a wani hari da aka kai wani kauye da ke arewa maso yammacin Kamaru.
Sama da rabin mutanen da aka kashe a Ntumbo yara ne, kuma kafafen yada labaran kasar sun ce wasu da dama sun kone kurmus.
Babu kungiyar da ta dauki nauyin kai harin na ranar Juma’a, sai dai jam’iyyar hamayya na zargin rundunar sojin kasar.
Gwamnatin Kamaru wadda take yaki da ‘yan aware a yankin kusan shekara uku kenan ta musanta hannu a harin.
James Nuna, wani jami’i daga hukumar ba da agaji ta MDD Ocha, ya fada wa BBC cewa wata mata mai juna biyu na daga cikin mutanen da aka kashe.
“Yara 14 ciki har da ‘yan kasa shekara biyar su tara, na daga cikin wadanda suka mutu,” a cewarsa.
Mr Nunan ya ce lamarin ya tayar da hankalin al’ummar yankin.
”Kowace kungiya ce ta yi haka ta yi barazanar kara tayar da hankali a gaba,” a cewarsa. ”Mutanen da muka yi magana da su sun kadu matuka kuma ba su yi tsammanin faruwar haka ba.”
Cikin wata sanarwa, daya daga cikin manyan jam’iyyun hamayyar kasar – MRC – ta zargi gwamnatin kama karya da kuma shugaban dakarun kasar da kai harin.
Agbor Mballa wani babba a kungiyar ‘yan awaren ya ce sojojin kasar ne da alhakin kai harin.
Wani jami’in soji kuma ya karyata zarge-zargen lokacin da kamfanin dillancin labaran AFP ya tambaye shi game da lamarin.
Kungiyoyin ‘yan aware sun fara kafuwa a 2017 bayan da sojoji suk afkawa masu zanga-zanga.
‘Yan awaren sun ayyana cin gashin kansu a sabuwar jihar Ambazonia, sai dai shugaban kasar Paul Biya ya bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.
Sama da mutum 3,000 ne suka mutu tun bayan barkewar rikici kuma kimanin mutum 70,000 ne sukarasa muhallansu.
Ana zargin gwamnatin Kamaru da cin zarafin bil adama a lokacin yaki kuma Shugaban Amurka Donald Trump ya tsame kasar daga wani shirin kasuwanci na musamman.
Gwamnati ta ce ‘yan awaren sun kashe farar hula da sojoji da dama amma babu kididdiga a hukumance kan yawan farar hula da ‘yan waren da sojoji suka kashe.

