Abin da kuke bukatar sani kan tsarin bizar Najeriya na 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan sabon tsarin bizar Najeriya na 2020

Hakkin mallakar hoto
@BashirAhmaad

–BBC Hausa

Image caption

An fara gabatar da tsarin bizar Najeriya na farko ne a 1958, wato zamanin mulkin mallaka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin bizar kasar na shekarar 2020 ga ‘yan kasa, sai dai abin tambayar shi ne, me hakan ke nufi?

Shugaban ya ce sabon shirin zai hada kan ‘yan Afrika ta hanyar gabatar da tsarin karbar biza yayin da aka iso kasar don takaitacciyar ziyara ga mutanen da ke da Fasfon kungiyar hada kan Afrika ta AU.

A cewar fadar shugaban kasar, sabon tsarin zai taimaka wajen kara habaka kasuwanci a Najeriya da kuma kwadaitar da masu zuba jari daga kasashen duniya da ma masu zuwa yawon bude ido, ba tare da kawo barazana ga harkokin tsaron kasar ba.

Hakkin mallakar hoto
@NGRPresident

Abubuwan da ya kamata ku sani game da bizar

An fara gabatar da tsarin bizar Najeriya na farko ne a 1958 – zamanin mulkin mallaka.

Shirin na bana wani yunkuri ne na aiwatar da shirye-shiryen tsaron iyaka na hukumar kula da shige da fice ta kasar na shekarar 2019 zuwa 2023.

Tsarin ya kunshi daukar bayanan matafiyi da suka shafi bizar da yake amfani da ita, da kuma neman bayanansa daga rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta kara yawan adadin rukunin bizar daga shida zuwa 79.

Hakkin mallakar hoto
@NGRPresident

Wani babban abu da ke da muhimmanci a tsarin shi ne, binciken fasahar zamani ga matafiya da gwamnatin ta ce tana sa rai zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma aniyar gudanar da lamura a bude da kuma kare yaduwar cin hanci da rashawa.

Sabon tsarin ya kuma kunshi abubuwa kamar haka:

  • Neman bayanai game da kan iyakoki da ake kira (MIDAS)
  • Amfani da dangwalen yatsa da sauran bayanai don maye gurbin tsohuwar bizar da ake amfani da ita
  • Tsarin bizar da zai kasance yana da alaƙa da APIS da za’a iya amfani da ita wajen aiwatar da bincike dangane da matafiyi a ciki da wajen Najeriya

More from this stream

Recomended