Mai kai wasiku ya boye wasiku 24,000 a gidansa

Jami'an gidan wasika

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana zargin tun shekarar 2003 ne mutumin ya ke ajiye wasikun a gidansa

‘Yan sanda a Japan sun sanar da fara binciken kan wani tsohon jami’in kai wasiku da ya ajiye dubban wasikun mutane a gidan sa ba tare da ya kai wa mutanen ba.

Hukumomi sun gano kusan wasiku 24,000 a gidan mutumin da ke yankin Kanagawa, a kusa da birnin Tokyo.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ba abayyana sunansa ba mai shekara 61, bai damu ya kai wasikun inda ya dace ba sannan ya fi sauran abokan aikinsa karsashi.

Tuni gidan wasika na Yokohama ya nemi afuwar jama’a tare da alkawarin aike musu wasikun nan ba da jimawa ba.

Reshen da mutumin ke aiki a matsayin shugaban masu kai sakwanni, ya shaidawa wakilin kafarsadarwa ta Kyodo cewa tun abara ne suka fara zargin akwai matsala bayan sun gudanar da bincike ta internet. Nan take mutumin ya amince da aikata ba daidai ba, ba kuma tare da bata lokaci ba aka kore shi daga bakin aiki.

Hukumomin gidan wasikar sun shigar da kara gaban hukuma ‘yan sanda, kan korafin batan sama da wasiku 1000 tsakanin watan Fabrairun 2017 zuwa Nuwambar 2019.

Wasu rahotannin sun ce ta yiwu tsohon mai kai wasikun, ya dade ya na ajiye wasikun mutane a gidansa tun shekarar 2003.

Idan aka gurfnar da shi gaban shari’a, aka kuma same shi da laifi zai biya tarar kusan Dala 4,600 kusan Naira miliyan biyu kudin Najeriya.

More from this stream

Recomended