
Tun bayan zaben 2015 da kuma barakar da ta kunno kai tsakanin Sanata Kwankwaso da Abdullahi Ganduje, kungiyar Kwankwasiyya ta soma samun matsala
Daya daga cikin tasirin kurkusa da wannan hukunci zai yi shi ne sauya fasalin kungiyar siyasar Kwankwasiyya, wacce tsohon gwamnan jhar, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kafa tun bayan komawarsa kan karagar mulkin jihar tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Wannan kungiya dai ta yi suna sosai a Najeriya, inda magoya bayan tsohon gwamnan kuma tsohon Sanata na mazabar Kano ta Tsakiya, ke tawassali da irin ayyukan ci gaba da suka ce shugaban nasu ya yi a wancan lokacin, domin kafa hujjar farin jinin da kungiyar take da shi a fagen siyasa.
Wasu daga cikin manyan mabiyanta sun koma bangaren Gwamna Ganduje.
Kafin su raba gari, Abdullahi Ganduje da Kwankwaso, sun yi mulkin jihar Kano tare, lokacin da Kwankwaso ke matsayin gwamna, Ganduje kuma mataimakinsa.
Wani abu da ya sake raba kan ‘yan kungiyar ta siyasa ta Kwankwasiyya shi ne matakin da Gwamna Ganduje ya dauka – lokacin da ya hau karagar mulkin jihar – na goge sunan ‘Kwankwasiyya’ daga gine-ginen gwamnati da suka hada da na makarantu da asibitoci da sauransu, wadanda tsohon Gwamna Kwankwaso ya rubuta – da alama domin ka da a manta da ayyukan da ya yi lokacin shugabancinsa.
Daga bisani kuma Gwamna Ganduje ya daina sanya jar hula, wadda ita ce alamar kungiyar, lamarin da ya sake bakanta ran mabiyan Sanata Kwankwaso.
Ba yau farau ba
Kazalika gabanin zaben 2019, wasu na-hannun daman Sanata Kwankwaso, wadanda suka hada da tsohon mataimakin Gwamna Ganduje, Hafiz Abubakar da kuma tsohon shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya, Aminu Dabo, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Amma wasu masana harkokin siyasa na ganin hukuncin da Kotun Kolin Najeriya ta yanke na yin watsi da karar da dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya shigar yana kalubalantar zaben Gwamna Ganduje, zai yi tasiri kan Kwankwasiyya fiye da duk sauran abubuwan da suka faru a baya.
Mutane da dama sun kalli fafutikar siyasa da shari’ar tsakanin Abba Kabir da Gwamna Ganduje tamkar fafatawa ce tsakanin Kwankwasiyya da ‘Gandujiyya’, wato tafarkin siyasar Gwamna Ganduje musamman ganin cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne kashin bayan siyasar PDP, da dan takararta Abba Kabir wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.
Rabi’u Sulaiman Bichi ya taba zama sakataren gwamnatin jihar Kano lokacin mulkin Kwankwaso
Hukuncin Kotun Kolin na nufin duk wani dan siyasa da ke boyon bayan tsohon Gwamna Kwankwaso zai ci gaba da yin azumin siyasa har a kalla zuwa shekarar 2023, lokacin da ake sa ran za a sake buga kugen siyasa.
‘Yan siyasar Najeriya na tsoron talauci
Amma wasu na ganin ai shekara kwana ce, yayin da wasu ke cewa siyasa ‘yar dabara ce, don haka akwai damar bangaren Kwankwasiyyar su sake nazari, su kuma kara shan damara domin yin amfani da kura-kuran gwamnatin Ganduje, domin su samu karin karbuwa da farin jini da kuma yin tasiri a jihar, ko da ba su kan karagar mulki a yanzu.
Sai dai kamar yadda dabi’ar ‘yan siyasar Najeriya take, galibinsu sun fi so suna tare da mai mulki domin tsoron talauci, don haka hukuncin kotun zai jarraba mabiya wannan kungiya ta Kwankwasiyya domin tantance ainihin karfin akidarsu da kuma juriyarsu a siyasance.
Tuni dai shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, wanda kuma jigo ne a kungiyar ta Kwankwasiyya, Rabi’u Sulaiman Bichi, ya sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Rabi’u Bichi ya tabbatar wa BBC fitarsa daga PDP zuwa APC ko da yake ya ce sai nan gaba kadan zai yi cikakken bayani kan dalilansa na sauya sheka.
Wani matashi dan jam’iyyar ta PDP, Salisu Yahaya Hotoro, ya ce masu rikon amana ya kamata a rika bai wa shugabanci a jam’iyyar.
Ya kuma yi kira ga jagoransu, Sanata Kwankwaso, ya gwada irinsu matasa domin ganin an samu shugabanci na “rashin cin amana.”
Sai dai masana harkokin siyasa irin su Kabiru Sa’idu Sufi, Malami a Kwalejin Ilimi da Share Fagen Shiga Jami’a (CAS) da ke Kano, ya ce ficewar shugaban jam’iyyar ta PDP a jihar Kano da wasu irinsa da ka iya biyo baya, za ta iya girgiza kungiyar da farko, “amma daga baya komai zai iya komawa daidai a tafiyar ta Kwankwasiyya.,” in ji shi.
Matasa na tare da Kwankwasiyya
“Da ma an yi hasashen faruwar ficewar wasu daga cikin PDPn Kano da ma kungiyar Kwankwasiyya, kuma da farko wannan mataki zai girgiza su amma dorewar wannan kungiyar zai dogara ne ga yadda jagoransu [Kwankwaso] zai gudanar da al’amuransa.
“Yana iya duba dalilan ficewar jigogin da niyyar magance hakan idan akwai dalili.
“Kada ka manta kuma akwai matasa da suka ci moriyar gwamnatin Kwankwaso inda aka kai wasu karatu kasashen waje sannan aka inganta rayuwar wasu.
“Da wahala wadannan matasa su daina mubaya’a ga Kwankwasiyya. Amma ka san yana da kyau a jam’iyya da kungiya akwai manya da za su yi jagoranci da kuma matasa da za su ingiza tafiya,” in ji Malam Kabiru Sufi.
Wasu masana kuma na ganin hukuncin Kotun Kolin ka iya sauya tunanin jama’a da yadda suke kallon dokokin zabe da tsarin shari’ar kasar.
Farfesa Jibrin Ibrahim, masanin kimiyar siyasa ya wallafa a shafinsa na Facebook jim kadan bayan yanke hukuncin, cewa: “Idan har ana son gudanar da sahihin zabe, dole ne ‘yan kasa su dauki matakan kare nasarar zabensu domin kuwa hukumomi ba abin dogaro ba ne.”
A halin da ake ciki dai za a ci gaba da bibiyar yadda tafiyar kungiyar ta Kwankwasiyya za ta kasance a bangare guda, da kuma yadda Gwamna Abdullahi Ganduje zai ci gaba da jan ragamar jihar a daya bangaren.
A karshe kuma, tsakanin bangarorin biyu, kowa ya iya allonsa sai ya wanke, yayin da jama’ar jihar musamman talakawa ke da matukar bukatar muhimman abubuwa da za su inganta rayuwarsu.