Rashford ya ji rauni a wasan kofin FA da kungiyarsa ta yi da Wolves makon da ya gabata
Inter Milan ta shirya biyan fam miliyan 11 ga dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen.(Sky Sports).
Ita kuwa Manchester United fam miliyan 43 ta ware don taya dan wasan gaban Lyon na Faransa Moussa Dembele bayan da Marcus Rashford ya samu rauni a baya.(Foot Mercato, via Manchester Evening News)
A wata mai kama da haka mai horar da yan wasan United din Ole Gunner Soskjaer ya sha suka saboda saka Rashford wasa bayan ya san da cewa yana da rauni a bayan nasa.
Shima tsohon dan wasan Manchester United Robin Van Persie ya ce bai kamata mai horar da ‘yan wasan ya yi gaggawar saka Rashford wasa ba, duk da yana da masaniya kan ciwon bayansa.(Manchester Evening News).
Christian Eriksen
Masana kamar irin su Ian Wright na ganin Soskjaer ya so kanshi, kuma ya jawo wa kansa matsala, ganin cewa dan wasan zai shafe akalla makonni shida yana jinya.
Haka ma wasu rahotanni sun ruwaito cewa an bukaci kungiyar da ke birnin Manchester da ta kara sabon tayi mai gwabi in har tana son sayen Edinson Cavani na PSG.(Manchester Evening News)
A Italiya ma cinikin Victor Moses da Inter Milan ya kusa fadawa, bayan da tsohon kociyansa Antonio Conte ya nuna sha’awar kawo shi.(Mail).
Tsohon mai horar da Arsena Arsene Wenger ya ce kungiyar ta hadu da cikas tun bayan barin tsohon filin wasa na Highbury zuwa sabon filin wasanta na Emirates.(Evening Standard).
Ita kuwa Liverpool ta ce ba ta shirya sayar da dan wasan tsakiyarta Xhendan Shaqiri ba, duk da kungiyar Roma ta Italiya na nemansa. (Sky Sports).