‘Yan bindiga ‘sun kashe mutum 29’ a Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Wasu ‘yan bindiga sun abka kauyen Babban Rafi da ke karamar hukumar Gummi a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wani mazauni garin ya shaida wa BBC cewa mutum 29 maharan suka kashe, yayin da kuma suka watse sauran mutanen garin da ya ce sun gudu zuwa wasu garuruwan jihar Kebbi.

“Sun ta bude wuta kuma ko wane mashin yana da dauke goyon mutum uku, suna bin mutane suna harbi suna kashewa. sun ci gari da yaki,” in ji shi.

Rundunar ‘Yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kai harin, amma kakakinta SP Mohammed Shehu ya shaida wa BBC cewa mutum 14 ne aka kashe, kuma ya ce maharan sun tsallako ne daga jihar Kebbi da ke makwabta da Zamfara.

Hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a domin neman kudin fansa na kara kamari a jihohin Zamfara da Katsina da ke arewa maso yammaci, duk da ikirarin gwamnatocin jihohin na yin sulhu da ‘yan fashi da barayin.

Wasu masu sharhi a kan harkokin tsaro a Najeriya sun yi gargadin cewa wasu `yan bindigar za su iya amfani da sulhun su mayar da shi wata hanyar tatsar gwamnati.

Tun a bara gwamnatin Zamfara ta ce ta yi sulhu da barayi da masu satar shanu da garkuwa da mutane.

More from this stream

Recomended