
Wani jirgi mallakar rundunar sojin Sudan ya yi hatsari a Yammacin Darfur, inda a kalla mutum 18 suka rasa rayukansu, ciki har da yara hudu.
Jirgin dai ya yi hatsari ne mintuna biyar bayan ya tashi daga wani filin jirgi da ke babban birnin Yammacin Darfur wato El Geneina.
Jirgin dai ya jima yana kai agaji a yankin wanda aka kwana biyu ana samun arangama tsakanin kabilun yankin.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Mohammed al-Hassan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa cikin wadanda suka mutu a hatsarin akwai ma’aikatan jirgin bakwai da alkalai uku da kuma fararen hula takwas, wadanda a ciki akwai kananan yara.
Babu dai wani cikakken bayani dangane da musababbin abin da ya jawo hatsarin.
Sai dai Mista Hassan ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.
A wannan makon, a kalla mutum 48 suka mutu inda kuma 241 suka samu raunuka a wani rikici da ya barke a Yammacin Darfur kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta Sudan Red Crescent ta bayyana.
An samu arangama ne tsakanin Larabawa da kuma kabilun ‘yan Afirka da ke El Geneina a daren Lahadi, inda rikicin ya ci gaba har rana ta gaba.