Laliga: Kalubalen da Lionel Messi zai fuskanta a 2020

Messi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana hasashen cewar sabuwar shekara ta 2020 za ta zama ta musamman ga Lionel Messi na Barcelona dan kwallon tawagar Argentina.

Shekara ce da ake gani Messi zai kara kafa tarihi a fanni da ya hada da cin kwallaye da lashe kofuna da yawan buga wasanni a Barcelona da dai sauransu.

Ganin haka ga wasu daga kalubalen da Messi zai fuskanta a 2020

Doke Pele a tarihin cin kwallaye a kungiya daya.

Pele ya ci kwallo 643 a kungiyar Santos a lokacin da ya taka leda, kawo yanzu saura 25 Messi wanda ya ci wa Barcelona kwallo 618 ya yi kan-kan-kan da Pele.

Lashe Champions League na biyar.

Bayan da kawo yanzu Messi ya yi shekara biyar ba tare da lashe kofin Champions League ba, hakan na nufin zai yi kishirwar kofin a 2020.

Hakan na nufin zai sa rana lashe Champions League na biyar a tarihi daga nan zai zama saura daya ya yi kan-kan-kan da Paco Gento mai shida jumulla a kofin Zakarun Turai.

Cin kofin La Liga na tara a cikin shekara 12.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tun lokacin da Messi ya fara buga wa babbar kungiyar Barcelona, sau biyar ne kacal ba ta ci kofin La Liga daga 16 da ta fafata ba.

Kawo yanzu yana da guda 10 a tarihi, yana fatan daukar na tara a shekara 12 da suka wuce.

Zama sarkin lashe kofuna a tarihi.

Babu kungiyar da ta kai Barcelona yawan lashe Copa del Rey da take da shi 30, sai Athletic Club mai 23.

Messi zai bukaci tarihi biyu a wannan fannin na farko dai yin kan-kan-kan da Jose Maria Belausate da Agustin Gainza wanda suka buga Copa Del Rey sau takwas kowannensu.

Na biyu kuwa shi ne na biyar wajen cin kwallaye a gasar, bayan Telmo Zarra mai 81 da Josep Samitier mai 69 da Guillermo Gorostiza mai 64 da Edmundo Suarez mai 55, sannan Messi mai 51.

Lashe kyautar Ballon d’Or na bakwai.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bayan da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shida jumulla a 2019, kuma shi ne kan gaba a tarihi, Messi zai so ya kara yin gaba wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya a 2020.

Dan wasan Barcelona kan gaba wajen buga El Clasico

Messi ya yi kan-kan-kan da Xavi wajen buga El Clasico 42 a Barcelona a watan Disamba da suka fafata a Camp Nou.

Da zarar ya kara buga El Clasico na gaba zai zama na daya a Barcelona wajen buga karawar ta hamayya.

Wanda ke kan gaba wajen yi wa Barcelona wasanni.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kawo yanzu Xavi ya buga wa Barcelona wasa 767 fiye da Messi wanda ya yi 705.

Messi zai iya buga wasanni fiye da Xavi a 2020 duk da cewa abu ne mai wahala, amma idan har rauni bai kawo wa Messi tsaiko ba, hakika zai wuce Xavi ya kuma dora a kan haka kafin 2021.

Dan wasan da ya lashe kofuna da yawa a kungiya daya.

Tsohon dan wasan Manchester United, Ryan Giggs shi ne kan gaba wajen lashe kofi 36 a kungiya daya, sai Vitor Baia da ya dauki 35 a Porto.

Kawo yanzu Messi ya lashe kofi 34 a Barcelona, yana bukatar uku a 2020 domin zama kan gaba a cin kofuna a kungiya daya a duniya.

Zama na daya a cin kwallaye a gasar Champions League.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Messi ya ci kwallo 14, biye da Cristiano Ronaldo a jerin wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Champions League.

Cikin shekarar nan za a fayyace ko Messi zai iya haura Ronaldo a wannan tarihin ko kuma sai a shekarar gaba.

Lashe kofi da tawagar Argentina a bana

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Argentina tana da damar lashe kofi a bana tare da Messi, idan sun shiga gasar Copa America a bana.

Gasar shekarar nan za a yi ta a Argentina da Colombia, hakan zai bai wa Messi da Argentina damar daukar kofin, bayan da aka ci Argentina a wasan karshe a 2015 da kuma 2016.

More from this stream

Recomended