Waiwaye kan Aisha Buhari a 2019 | BBC Hausa

@AISHAMBUHARI

Hakkin mallakar hoto
@AISHAMBUHARI

Tun a farkon shekarar 2019, uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karyata wasu rahotanni da suka ce ta yi Allah wadai da dakatar da Walter Onnoghen, wanda shi ne Alkalin Alkalan Najeriya.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun daraktan watsa labaranta Suleiman Haruna, ta bayyana cewa labarin da ake yadawa a kafofin sadarwa cewa ta yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen ba gaskiya ba ne.

A watan Maris din shekarar 2019, Aisha Buhari ta ja kunnen ‘yan jam’iyyar APC kan cewa idan an zo rabon mukamai, to a raba su ga masu rike da katin jam’iyya.

Hajiya Aisha ta bayar da wannan shawara ce a wajen wata liyafar cin abincin dare da aka gudanar a Daura, kwanaki kadan bayan mai gidanta Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019.

Hajiya Aisha ta ce, kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bayyana karara cewa masu katin jam’iyya kawai za a dinga bai wa mukamai, “a don haka ne ya kamata jam’iyya ta girmama kundin tsarinta kamar yadda ya dace.”

Haka zalika yayin wani taron girmama matan tsofaffin gwamnoni a watan Yuni, Aisha Buhari ta yi gargadin cewa ka da wanda ya kara kiranta da lakabin ‘Matar Shugaban Kasa’, sai dai “Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady”.

Hakkin mallakar hoto
@AISHAMBUHARI

Ta ce ta zabi a kira ta da “Matar Shugaban Kasa” ne don radin kanta duk da cewa ya haddasa rudani.

Sai kuma babban abin da ya ja hankali dangane da Uwar Gidan Shugaban Kasar wato Aisha Buhari, shi ne rudani da aka shiga a Najeriya kan zargin da ake yi na cewa mai gidanta Muhammadu Buhari zai kara aure,Muhammadu Buhari zai kara aure, a watan Oktoba.

An ta yada hotunan bogi da kuma katin daurin aure na bogi a shafukan sada zumunta wanda fadar shugaban kasar ta karyata.

Hakan duk ya faru ne yayin da Aisha Buhari ke Ingila inda ake zargin ta yi yaji wanda ta musanta hakan.

A yayin da ta isa Najeriya, ta fadi kalamai da suka bayar da mamaki kuma suka jawo ce-ce-ku-ce.

Aishar ta yi karin haske dangane da wani bidiyo da ya rinka yawo a shafukan sada zumunta wanda a cikinsa aka ga uwargidan shugaban Najeriyar tana ta fada da harshen Turanci tana gaurayawa da Hausa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun rinka alakanta wannan bidiyon da cewa Aisha Buhari ce ta dawo daga Ingila tana fada cewa an rufe mata kofa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanin Aisha Buhari kan bidiyon Fadar Shugaban Najeriya

BBC ta samu jin ta bakin Aisha Buhari inda ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

Ta kuma yi karin haske cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta nadi bidiyon da ake tafka mahawara a kai.

Sai dai ko da BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta musanta daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Martanin Fatima Mamman-Daura
  • Mahaifina bai kanainaye gwamnatin Buhari ba —Fatima Mamman Daura
  • ‘Mai karfin fada a ji’, wane ne Mamman Daura?

Jim kadan bayan wannan batu ya yi sanyi, sai kuma kan batun taron addu’o’i na musamman da aka gudanar a fadar shugaban kasa a watan Nuwamba, wanda matar shugaban kasar ta kira domin neman agajin Ubangiji game da tarin kalubalen da kasar take fuskanta.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/AISHA BUHARI

Wasu ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun rinka muhawara, ganin cewa taron ya hada malamai daga kungiyoyi daban-daban na addinin musulunci na kasar, wadanda ke da banbancin fahimta game da asali ko rashinsa na bikin maulidi.

  • Hotunan malamai a wajen taron Aisha Buhari na addu’a

Sai dai a wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Aisha Buhari kan yada labarai, Aliyu Abdullahi ya fitar, ta ce an shirya taron ne don yin duba kan muhimmancin addu’o’in nemar wa Najeriya ci gaba, ba tare da alakanta shi da bikin maulidi ba.

Amma a lokacin da take nuna rahoton, kafar yada labaran talbijin ta kasar wato NTA, ta sanya rubutu ta kasa cewa “Ranar Maulud: Aisha ta hada taron addu’ar kasa,” duk da dai ba a ambaci haka a rahoton ba.

Hakkin mallakar hoto
THISDAYLIVE

Sai kuma a watan Disambar 2019 ne uwar gidan shugaban kasar ta wallafa wani rubutu inda da kanta ta caccaki mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu.

Rubutun da aka wallafa mai taken “Garba Shehu na wuce gona da iri”, mai dakin Shugaba Buharin ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke ‘yi wa iyalan shugaban zagon kasa’.

Aisha Buhari ta ce “Garba Shehu na daya daga cikin masu kware wa Buhari baya kasancewar yaron abokin hamayyar Buharin ne a zaben shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.”

To sai dai da BBC ta tuntubi Malam Garba Shehu kan batun, ya ce ba zai sa-in-sa da mai dakin mutumin da yake yi wa aiki ba.

More from this stream

Recomended