
Akwai wasu bayanan da ba na gaskiya ba da ke kai komo a shafukan sada zumunta dangane da al’aurar mata, kuma wata mace ta dauki gabarar gyara irin wannan tunanin.
Dr Jen Gunter, wadda likitar mata ce ta kwashe shekaru 25 tana aikin kula da lafiyar mata a Amurka da Canada. Har wa yau, ana bayyana Dr Jane mai fafutukar lafiyar mata a shafukan Twitter.
A baya-bayan ta tunkari wani ikrari da ke cewa cusa kwai mai tauri a cikin al’aurar mace na taimakawa wajen samun daidaito a lokacin al’ada da kuma sarrafa mafitsara.
Dr Jane ta nuna cewa ikrarin sam ba ya cikin tsaffin al’adun mutanen kasar Sin kuma ba su da madogara a kimiyyance. Hakan ya sa aka yi wurgi da ikrarin.
Littafin Dr Gunter da ta wallafa a baya-bayan nan shi ne ‘The Vagina Bible’ wato Kundi kan abin da ya shafi al’aurar mata, ya kasance littafin da aka fi rububin nema a kasashe da dama.
Littafin na kunshe da shawarwari na hakika domin kara wa matan sani kan yadda za su inganta rayuwarsu. Dr Jane ta zayyana wasu abubuwa da take ganin ya kamata duk wata mace ta sani.
Hakkin mallakar hoto
Emma Russell
1 – Muhimmancin sanin al’aura tun daga dunbaru
Ita al’aurar mace na cikin jikinta ne, wato wata kafa ce da ta hada mahaifar mace da wajen al’aurarta. Fatun da ke taba fatarin mace su ne ake kira da dunbaru.
Gunter na da fahimtar cewa sanin banbanci tsakanin abubuwan guda ka iya taimaka wa mata wajen sanin hakikanin abin da ke damun su idan suka samu larurar da ta shafi matantaka.
2 – Al’aura na tsaftace kansa
Gunter ta fajimci cewa an samu sauyi a shekaru 10 da suka gabata, inda da dama daga cikin mata ke amfani da wasu abubuwa domin kyautata kamshin gabansu.
Kusan kaso 57 da matan North America suke wanke gabansu a ‘yan shekarun da suka gabata, inda wasu ke fadin mazajensu ne ke ba su shawar yin hakan.
To sai dai Gunter ta ce babu bukatar yin amfani da wani abu domin wanko cikin al’aurar mata.
“Wani bututu ne da ke wanko kansa,” in ji Gunter.
Gunter ta kuma yi gargadi kan amfani da abubuwa masu kanshi.
“Ita al’aurar mace ba ta son bako.”
Ko da ruwa ka iya kawo cikas ga tsarin halittar gaban mace, ta hanyar janyo kamuwa da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i. Shi ma turaren da ake yi wa al’aura ka iya janyo konewarsa.
Ana iya amfani da ruwa wajen tsaftace dunbaru idan har ya zama dole.
Yin amfani da sabulu ka iya debe yadin fata wanda ke yi wa fatar dan adam garkuwa. Idan mace ta kai shekarun daukewar jinin al’ada, za ta iya amfani da man kwakwa ko kuma na zaitun.
Ana samun sauyin kwayoyin halittar farjin mace a duk awa 96, fiye da sauyin da fata take samu a sauran sassan saboda haka za su fi saurin samun waraka.
Hakkin mallakar hoto
Emma Russell
3 – Al’aura tamkar lambu ne
Gaban mace na kunshe da kwayoyin bacteria ‘masu kyau’ da ke bayar da kariya ga al’aurar.
“Al’aurar mace kamar lambu ne mai dauke da kwayoyin bacteria iri-iri da ke aiki tare don tabbatar da cewa al’aurar na da koshin lafiya,” in ji Gunter.
Kwayoyin bacteria ‘masu kyau’ na samar da yanayi mai dan zafi, wanda ke hana kwayoyin bacteria ‘marasa kyau’ samun wurin zama, da kuma majina da ke tabbatar da cewa al’aurar ta kasance a jike ko yaushe.
Shi ya sa goge cikin al’aura da jikakken tsumma ba shi da amfani- yana da amfani ta kasance da kwayoyin bacteria ‘masu kyau’. Haka kuma, Gunter ta bayar da shawarar cewa a daina amfani da injin bushar da gashi wajen busar da al’aura: ana bukatar fatar al’aura ta kasance a jike.
Hakkin mallakar hoto
Emma Russell
4- Akwai dalilin da ya sa aka halicci gashi a jikin al’aura
Gunter ta lura cewa akwai karuwar mata masu aske gashin jikin al’aurarsu. Wannan na taimkaawa wajen hana kwarkwata yaduwa a wajen, amma akwai hadari a tattare da hakan.
“Idan aka aske ko aka cire gashin, kina jin ciwo a fata,” in ji Gunter. “Muna ganin yanka ko kujewa har ma ya zama gyambo idan aka cire gashin al’aura.”
Gunter ta ce idan za a yi aski, a yi amfani da reza mai tsafta sannan a gyara fatar wajen yadda ya kamata.
Kuma Gunter na son mutane su san matakan da suke dauka.
“Gashin da ke jikin al’aura na da amfaninsa, babu mamaki wata garkuwa ce kuma kariya ga fatar wurin,” in ji ta.
“Haka kuma, akwai yiwuwar cewa yana taka rawa wajen saduwa saboda ko wane silin gashi daya na hade ne da wata jijiya- shi ya sa idan ana tsige shi yake zafi.”
5- Tsufa na shafar al’aura
Bayan tsawon shekaru ana jinin al’ada da haihuwa, mace na kaiwa shekarun daukewar al’ada. Yawan sinadaran dake sa mace daukar ciki na yin kasa sosai- kuma raguwar sinadarin oestrogen na shafar al’aura da dumbaru.
Wadannan abubuwan, wanda a da majina ke sawa su zama a jike na iya kankancewa, ko kuma su jawo bushewar al’ada. Wannan na iya sa wa mace ta rika jin zafi lokacin saduwa.
Wannan na iay jefa mace cikin tsananin damuwa, amma Gunter ta ce mafi yawan mata na iya neman taimako daga wajen likita. Kuma wasu na iya sayen mayukan da ake shafawa a al’aura domin ta jike.
“Ina ganin yana da matukar muhimmanci idan mata suka san haka,” in ji ta. “Ba sai kin wahala ba.”