An zargi Senegal da cogen shekarun matasa ‘yan kwallo | Sport news

Brazil

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Senegal ta yi watsi da zargin da ake mata na cogen shekarun ‘yan kwallo matasa ‘yan 17, bayan da ta bayyana wadanda za su wakilce ta a gasar kofin duniya.

Kasar Brazil ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 da za a fara ranar 26 Oktoba a kammala ranar 17 ga watan Nuwamba.

Senegal ta samu wannan gurbin ne daga hudun da za su wakilci Afirka a kofin duniyar, bayan da aka kori Guinea, sakamakon an sameta da laifin cogen shekarun ‘yan wasa a gasar Afirka.

Hukumar kwallon kafar Senegal ta ce babu wani dan kwallo da ke buga wa babbar tawagar kasar tamaula da aka gayyata zuwa Brazil.

Ana ta watsa jita-jita a kafar sada zumunta cewar Senegal ta kira ‘yan wasa da dama da suka yi karyar shekarunsu na haihuwa.

Hukumar kwallon kafar Senegal ta ce ‘yan wasanta sun yi gwajin tantance shekarun haihuwa a gasar nahiyar Afirka, kuma Fifa za ta yi na ta daga 22 ga watan Oktoba zuwa 24 a Brazil.

‘Yan wasa uku kacal Senel ta canja daga wadanda suka buga mata wasannin nahiyar Turai na matasan.

Wadanda aka ajiye sune El Hadji Gueye da Meleye Diagne da kuma Ousmane Diallo, yayin da aka maye gurbinsu da Mamadou Aliou Diallo da Mbaye Ndiaye da kuma Ibrahima Sy.

Sauran kasashen da za su wakilci Afirka a gasar ta matasa ta duniya a Brazil sun hada da Kamaru wadda ta lashe kofin Afirka da Najeriya da kuma Angola.

Senegal wadda tuni tana Brazil tana shirye-shiryen karawa a rukuni na hudu da ya hada Amurka da Japan da kuma Netherlands.

Matasan ‘yan wasan tawagar Senegal :

Masu tsaron raga: Ousmane Ba (Generation Foot), Mamadou Aliou Diallo (Diambars FC), Pape Ibrahima Dione (AF Darou Salam)

Masu tsaron baya: Thibaut Aubertin (Generation Foot), Cheikh Mbaye Diouf (Diambars FC), Bacary Sane (Diambars FC), Cheikhou Oumar Ndiaye (Generation Foot), Mikayil Ngor Faye (Diambars FC)

Masu wasan tsakiya: Amete Saloum Faye (Diambars FC), Boubacar Diedhiou Diallo (Diambars FC), Issaga Kane (Galaxy FA), Ibrahima Cissokho (US Goree), Pape Matar Sarr (Generation Foot), Insa Boye (Diambars FC)

Masu wasan gaba:Aliou Badara Balde (Diambars FC), Souleymane Faye (Galaxy FA), Mouhamadou Moustapha Diaw (Diambars FC), Samba Diallo (AF Darou Salam), Birame Diaw (Galaxy FA), Mbaye Ndiaye (Dakar Sacre Coeur), Ibrahima Sy (Reims, France)

Related Articles