Za a debo ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu a kyauta

Rikicin Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wadannan rikice-rikicen kin jinin baki a Afirka ta Kudu ba

An yi wa ‘yan Najeriya da ke Afirka ta Kudu tayin jirgin sama kyauta don dawowa gida “bayan rikice-rikicen nuna kin jinin baki na baya-bayan nan da suka barke a kasar”, a cewar ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya.

Ma’aikatar ta ce mamallakin kamfanin jiragen saman na Air Peace ya ce zai bayar da jirgi kyauta a kwaso ‘yan Najeriya ranar Juma’a.

Sanarwar ma’aikatar ta ce “Yan Najeriya da ke sha’awar dawowa gida na iya tuntubar ofishin jakadancin Najeria a birnin Pretoria da Johannesburg domin shirye-shiryen da suka dace.”

Harin da aka kai wa shaguna da wuraren sana’a na baki a Afirka ta Kudu ya tunzura ‘yan Najeriya da dama da ke ganin ba a yi adalci ba.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Laraba cewa bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a kashe dan Najeriya ko daya ba a rikicin.

Sai dai ya ce gwamnatin na duba yiwuwar yi wa jakaden kasar a Afirka ta Kudu kiranye tare da neman diyya ga sana’o’in Najeriya da aka lalata.

Najeriya dai ta janye daga Taron Tattalin Arziki na duniya da ke gudana a Afirka ta Kudu a wannan makon bisa hare-haren.

Ta gargadi ‘yan kasarta daga “ziyartar wuraren da rikici ka iya barkewa” a Afirka ta Kudu har sai an samu zaman lafiya.

Ita kuma Afirka ta Kudu ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya na wucin gadi bisa harin ramuwar gayya da aka kai a Najeriyar.

Tun ranar Lahadi, gungun mutane sun fasa shagunan baki a Afirka ta Kudu tare da sace kayan da ke cikinsu a birnin Johannesburg.

Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce abin kunya ne ga kasarta.

Mis Pandor ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ta umarci a rufe ofishin jakadancin kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya da Legas bayan barazana da aka yi ga ma’aikatansu.

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai aika manzo Afirka ta Kudu don nuna rashin jin dadin ‘yan Najeriya bisa tarzomar.

More from this stream

Recomended