Za a debo ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu a kyauta

Rikicin Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wadannan rikice-rikicen kin jinin baki a Afirka ta Kudu ba

An yi wa ‘yan Najeriya da ke Afirka ta Kudu tayin jirgin sama kyauta don dawowa gida “bayan rikice-rikicen nuna kin jinin baki na baya-bayan nan da suka barke a kasar”, a cewar ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya.

Ma’aikatar ta ce mamallakin kamfanin jiragen saman na Air Peace ya ce zai bayar da jirgi kyauta a kwaso ‘yan Najeriya ranar Juma’a.

Sanarwar ma’aikatar ta ce “Yan Najeriya da ke sha’awar dawowa gida na iya tuntubar ofishin jakadancin Najeria a birnin Pretoria da Johannesburg domin shirye-shiryen da suka dace.”

Harin da aka kai wa shaguna da wuraren sana’a na baki a Afirka ta Kudu ya tunzura ‘yan Najeriya da dama da ke ganin ba a yi adalci ba.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Laraba cewa bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a kashe dan Najeriya ko daya ba a rikicin.

Sai dai ya ce gwamnatin na duba yiwuwar yi wa jakaden kasar a Afirka ta Kudu kiranye tare da neman diyya ga sana’o’in Najeriya da aka lalata.

Najeriya dai ta janye daga Taron Tattalin Arziki na duniya da ke gudana a Afirka ta Kudu a wannan makon bisa hare-haren.

Ta gargadi ‘yan kasarta daga “ziyartar wuraren da rikici ka iya barkewa” a Afirka ta Kudu har sai an samu zaman lafiya.

Ita kuma Afirka ta Kudu ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya na wucin gadi bisa harin ramuwar gayya da aka kai a Najeriyar.

Tun ranar Lahadi, gungun mutane sun fasa shagunan baki a Afirka ta Kudu tare da sace kayan da ke cikinsu a birnin Johannesburg.

Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta ce abin kunya ne ga kasarta.

Mis Pandor ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ta umarci a rufe ofishin jakadancin kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya da Legas bayan barazana da aka yi ga ma’aikatansu.

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai aika manzo Afirka ta Kudu don nuna rashin jin dadin ‘yan Najeriya bisa tarzomar.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...