An sa dokar ta-baci a Sudan bayan kashe mutum 16 a Sudan

Jami'an tsaron Sudan

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Sudan ta yi fama da tarzomar masu neman tabbatar da mulkin dumokuradiyya tsawon watanni

Gwamnatin rikon-kwarya ta Sudan ta kafa dokar-ta-baci a yankin gabashin kasar, bayan wani rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16.

Haka kuma gwamnatin ta wucin-gadi ta kori gwamnan jihar Red Sea, tare da babban jami’in tsaro na yankin.

Ba a dai san ainahin abin da ya haddasa rikicin ba, zuwa yanzu.

Wata sanarwa ta gwamnati ta ce a karon farko a irin wannan rikici, an yi amafani da bundugogi, abin da ke nuna alamun sanya hannun wasu na ciki da wajen kasar domin rura wutar rikicin.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

A tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban Sudan Omar el Bashir wani jami’in tsaro ya ce ya amshi miliyoyin daloli daga Saudiya

A ‘yan kwanakin nan ne dai Sudan din ta fito daga rikici na wata da watanni,

inda aka yi yarjejeniyar kafa gwamnatin riko ta raba iko tsakanin farar-hula da soji, bayan kawar da gwamnatin dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir.

Daga cikin muhimman ayyukan da ya fara sabon Firaministan kasar ya ce ya fara tattaunawa da Asusun Lamuni na Duniya IMF, da Bankin Duniya a wani yunkuri na sake fasali ga dimbin bashin da ake bin Sudan din.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Janar Burhan ne zai jagoranci gwamnatin hadaka a watanni 21 na farko a Sudan

A yayin wata hira da kamfanin dillacin labarai na Reuters Abdallah Hamdok ya ce Sudan tana kuma neman tallafin dala biliyan 8 daga kasashen duniya nan da shekara biyu, da kuma wani tallafin gaggawa a yanzu domin karfafar darajar kudin kasar.

Tashin farashin mai da na abinci ne dai suka haifar da zanga-zanga a watan Disamba, abin da ya yi sanadin hanbarar da Shugaba Omar Albashir, wanda yanzu yake fuskantar shari’a a kasar.

More from this stream

Recomended