Tsawa ta rufta wa babban ofishin ‘yan sandan Wukari

Tsawa ta fada wa babban ofishin ‘yan sandan Wukari da ke jihar Taraba yayin da ake tafka ruwa a daren Alhamis. Duk da dai babu wanda ya raunata, tsawar ta hallaka wata katuwar bishiya da ke gaban ofishin ‘yan sandan.

Wasu ‘yan sanda da ke kan aiki a lokacin da tsawar ta fada wa gurin sun ce karar gagaruma ce da har ta sa kowannensu ya nemi mafaka.

Wani dan sanda da ya nemi kar a bayyana sunansa ya bayyana wa Daily Trust cewar Allah ya takaita babu wani mutum ko abin hawa a kasan bishiyar a lokacin da tsawar ta fado.

More from this stream

Recomended