
Hakkin mallakar hoto
Allure
Jarumar fina-finan Bollywood Priyanka Chopra, ta wallafa sakon tayin murnarta ga Gimbiya Meghan Markle da kuma Yarima Harry dangane da samun karuwar da da suka yi.
Priyanka, ta wallafa sakon ne a shafinta na Instagram inda ta yi musu murna tare da sanya hoto a shafin nata.
Tauraruwar ta yi rubutu kamar haka, ‘Ina mai matukar taya M da H murnar samun karuwar da namiji’.
Priyanka dai kawa ce ga gimbiyar tun kafin ta yi aure.
Hakkin mallakar hoto
Page Six
Ko a lokacin bikin Yarima Harry da Gimbiya Meghan, Priyanka ta kasance daga cikin manyan kawayen amarya.
A ranar Litinin 6 ga watan Mayu, 2019, ne aka haifi jaririn wanda shi ne zai zama na bakwai a jerin mutanen da ka iya gadon sarauniya, bayan yariman Wales, da Yariman Cambridge da ‘ya’yansa – Yarima George, da Gimbiya Charlotte da kuma Yarima Louis, sai kuma Yariman Sussex.
Sabon jaririn zai zama tattaba kunen saurauniya na takwas.