Chrishanthini wata malama ce wadda ta rasa iyayenta a yakin basasar da aka yi a Sri Lanka, kuma a yanzu ta kara rasa mijinta.
Malama ce a makaranta a gabashin kasar.
An kashe mijinta Ramesh a cocin Zion da ke Batticaloa bayan ya fitar da wani mutum mai dauke da wata jaka daga cocin.
A kalla mutum 25 sun mutu a yayin fashewar bam din, a cikinsu har da yara 13.