A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La Liga wasan mako na 35, inda Barcelona za ta karbi bakuncin Levante.
A wasan farko da suka kara a gasar ranar 16 ga watan Disambar 2018, Barcelona ce ta yi nasara da ci 5-0.
Wadanda suka ci wa Barca kwallayen sun hada da Luis Suarez da Gerard Pique da kuma Lionel Messi wanda ya ci uku rigis a karawar.
Tun a ranar Laraba aka sa ran kungiyar ta Camp Nou za ta daga kofin La Liga, bayan da ta doke Alaves 2-0, sai dai kuma Atletico Madrid da ta ci Valencia 3-2 ya sa sai ranar Asabar za a mallaka mata kofin.
A wasan da Barcelona za ta karbi bakuncin Levante shi ne zai sa ta lashe kofin La Liga na bana da zarar daya daga abu uku ya faru ranar Asabar.
- Idan Atletico ta yi rashin nasara a karawa da Real Valladolid, za a bai wa Barcelona kofi tun kan ta fafata da Levante, da yake Atletico ce za ta fara yin wasa.
- Idan Atletico ta yi canjaras da Valladolid a ranar Asabar, ita ma Barca na bukatar canjaras ta lashe kofin La Liga na shekarar nan.
- Idan kuma Atletico ta ci wasanta ranar Asabar, ita ma Barcelona na bukatar doke Levante da zai sa a mika mata kofin La Liga na 26 jumulla.
Lionel Messi na Barcelona shi ne kan gaba da ya ci kwallo 33 a gasar La Liga, sai Karim Benzema na Real Madrid da Luis Suarez na Barcelona da kowanne keda 21 a raga.
Wasannin mako na 35 ranar Asabar 27 ga watan Afirilu.
- Athletic de Bilbao da Deportivo Alaves
- Atletico de Madrid da Real Valladolid
- Leganes da Celta de Vigo
- Barcelona da Levante
Karawar ranar Lahadi 28 ga watan Afirilu
- Valencia da SD Eibar
- Girona da Sevilla
- Real Sociedad da Getafe
- Villarreal da Huesca
- Rayo Vallecano da Real Madrid
Fafatawar Litinin 29 ga watan Afirilu
Barcelona tana mataki na daya a kan teburi da maki 80, sai Atletico Madrid ta biyu mai maki 71, yayin da Real Madrid ta hada maki 64, ita ce ta uku a teburin na La Liga.
Kungiyar ta Nou Camp na fatan lashe kofi uku a bana, inda za ta fafata da Liverpool a wasan daf da karshe a Champions League, sannan ta kai karawar karshe a Copa del Rey.