
Wasu ma’aurata a Carlifonia sun samu afuwar ‘ya’yansu bayan kotu ta same su da laifin azabtarwa da jefa yaran cikin yunwa shekara da shekaru.
Yaran David da Louise Turpin sun shaida wa Kotu cewa suna matukar kaunar iyayensu duk da cin zarafin da suka sha a hannu su.
A cikin watan Janairun bara aka cafke iyayen lokacin da ‘yar su mai shekara 17 ta tsere daga gidansu da ke Perris.
Iyayen sun amsa laifin da aka tuhume su da shi kan 12 daga cikin ‘yaransu 13 a tsawon shekara 9.
David-Louise Turpin/Facebook
The couple’s Facebook page contained numerous family photos
Iyayen za su shafe tsawon rayuwarsu a kurkuku, sai dai idan an yi musu afuwa a cikin shekaru 25.
Me yaran suka ce?
Ma’auranta sun fashe da kuka lokacin da suka ji irin bayanan da ke fito wa daga bakin hudu daga cikin yaran na su a lokacin sauaron karar.
”Ina matukar kaunar iyaye na sosai,” kalaman daya daga cikin yaran kenan.
”Duk da cewa ana ganin yanayin su na tarbiyar damu bai dace ba, na ji dadin irin salon tarbiyatarwar su saboda a yau ina alfahari da mutumin da na zama.”
AFP
David Turpin ya fashe da kuka lokacin da aka yanke masa hukunci
Shi ma daya cikin yaran ya bayyana irin halin da wannan al’amari ya jefa su.
”Ya ce ba zan iya bayanan irin halin da muka shiga ba lokacin da muke tasowa.”
”Wani lokaci ina mafarkin abubuwan da suka faru, ina hango yadda aka rinka daure ‘yan uwa na da dukan da suka sha.
”Abu ne da ya riga ya wuce yanzu lokaci ne na fuskantar zahiri.
”Ina son iyayena kuma na yafe duk abubuwan da suka yi mana.”
Sai dai ba dukkanin yaran ba ne ke da ra’ayi guda kan sassantawa ba.
Wata diyarsu, ta girgiza kai, ta ce: “Iyaye na sun sace mu kuruciyata, amma yanzu lokaci ne na fanshewa.
AFP
Louise Turpin na ta murmushi a Kotu
”Ni ‘yar gwagwarmaya ce, Ina da juriya kuma ba na karaya.”
Ta kara da cewa: ”Mahaifina ya sauya mahaifiyata. Sun kusan sauya ni nima, sai dai na yi saurin gano abin da ke faruwa.”
Me iyayen ke cewa?
David da Louise Turpin sun zub da hawaye sosai suna neman afuwar yadda suka ci zarafin yaransu.
A lokacin da ya ke jawabi a madadin mahaifin na su mai shekara 57, lauyan Tupin ya ce: ”Bani da niyyar cutar da ‘ya’ya na kuma na basu wannan tarbiyarce da zuciya guda’
”Ban azabtar da su ba kuma ba ni da niyyar cutar da ‘ya’ya na.
” Ina matukar son su kuma ina da yakinin cewa yara na na kaunarta.”
Getty Images
David da Louise Turpin
A lokacin da take yiwa kotu bayani, mahaifiyarsu Louise Turpin mai shekara 50, ta ce ayi mata afuwa kan abubuwan da ta aikata.
”Ina son yara na sosai,” ta ce, ”Burina a kullum shi ne na gansu, na rungume su na kuma nemi afuwarsu.”
Yaran David da Louise Turpin sun shafe shekaru suna fuskantar cin zarafi
Wani irin azabtarwa yaran suka sha?
lokacin da ‘yansanda suka kai samam gidan yaran da shekarunsu ke tsakanin 2 zuwa 29 na cikin yunwa.
Akwai dan su mai shekara 22 da aka sawa mari aka garkame shi a bakin gado. ‘Yan uwansa mata biyu kuma an sake su daga dauri.
An haramta musu wanka sama da sau daya a shekara, ba sa iya amfani da makewaye kuma babu wanda aka taba kai wa wankin hakori.
DAVID-LOUISE TURPIN/FACEBOOK
Da dama daga cikin yaran sun ce sun yafewa iyayen nasu