Shin an samar da tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna? – BBC Hausa

Sanda

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana ci gaba da samun rahotanni da ke cin karo da juna kan ikirarin da jami’an tsaro suke yi cewa sun tabbatar da tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Babbar hanyar ta yi kaurin suna wajen sace-sace mutanen don neman kudin fansa, inda mahara suke cin karen su babu babbaka.

Kabiru Adamu wato wani masani kan harkokin tsaro a kasar ya ce an sace kimanin mutanen 200 a babbar hanyar a watanni hudu na farkon wannan shekarar.

Amma akwai wadanda suke ganin adadin mutanen ya wuce hakan.

Galibin matafiya da ke zirga-zirga a hanyar yanzu suna amfani ne da jirgin kasar ne, maimakon motoci da suka saba amafani da su a baya.

A makon da ya wuce ne jami’an tsaro a kasar suka ce sun tabbatar da tsaro a wannan babbar hanyar.

Wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya kai ziyara babban tashar mota ta unguwar Jabi a Abuja don jin ta bakin wasu direbobi da fasinjoji kan ikirarin na jami’an tsaron.

More from this stream

Recomended