
A yayin da ake cigaba da hasashen takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a zaɓen shekarar 2027 sai gashi Jonathan ya ziyarci jagororin jam’iyar haɗaka ta ADC.
Ana ranar Alhamis ne Jonathan ya ziyarci shugaban jam’iyar ta ADC, David Mark a gidansa dake Abuja.
Ganawar na zuwa ne yan sa’o’in kadan bayan da gamayyar wasu yan siyasa da suka fito daga jam’iyyu daban-daban suka zaɓi jam’iyar ADC a matsayin sabuwar jam’iyar da za su kalubalaci jam’iyar APC da ita a zaɓen 2027.
Tuni dai wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyar adawa ta PDP suka fara zawarcin Jonathan kan yazo ya yiwa jam’iyar takarar zaɓen shugaban a zaɓen 2027.
Kawo yanzu dai babu wata sakarwa da aka fitar kan abun da ganawar ta mayar da hankali akai.