2027: Atiku Zai Koma APC Idan Tinubu Ya Yi Alkawarin Mika Masa Mulki — A Cewar Hadimin Wike

Mai magana da yawun Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya bayyana cewa duk wata ƙungiyar adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta za ta gaza tun daga farko.

Olayinka ya ce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai yi watsi da adawa ya koma jam’iyyar APC muddin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa alkawarin mika masa mulki a shekarar 2027.

Ya fadi hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi ba’a da Atiku bayan ziyararsa ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Kaduna.

A cikin tawagar Atiku da suka kai ziyara akwai tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal da tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswam.

Atiku ya ce dalilin ziyarar tasa shi ne domin kai gaisuwar Sallah ga Buhari. Sai dai Olayinka ya soki hakan, yana mai cewa Atiku da gaske ne yana son kai gaisuwa, to ya je Abeokuta ya gaishe da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo domin bikin Lisabi Day.

More from this stream

Recomended