Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi ya sanar da aniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Kawo yanzu dai Amaechi ne mutum na farko cikin masu rike da mukami a gwamnatin Buhari da ya fito fili ya nuna shaawarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Amaechi ya sanar da bukatarsa ta sa ne a yayin wani babban taron addu’ar godiya ga Allah da yayan jam’iyar APC na jihar Rivers suka shirya a Fatakwal babban birnin jihar.