Shugaban majalisar dattawa sanata, Ahmad Lawan ya roki yan Najeriya da su sake bawa jam’iyar APC dama a zabe mai zuwa.
Ya fadi haka ne a wurin taron jin ra’ayin jama’a da sanata mai wakiltar mazabar Kwara ta tsakiya, Dr Ibrahim Yahaya Oloriegbe ya shirya a ranar Asabar.
A wurin taron da ya gudana a birnin Ilorin Oloriegbe ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.
Tun da farko sai da shugaban majalisar dattawan ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da sanatan ya samar a mazabarsa.
Amma kuma Lawan ya gargadi mutanen jihar da su kaucewa dawo shugabannin da suka mulki jihar a baya.
“Ina son na yi kira ga dukkanin yan Najeriya da su sake bawa jam’iyar APC dama a dukkanin mataki har bayan 2023. Munyiwa yan Najeriya alkawarin cigaba da yin bakin ƙoƙarin mu. Kuma baza mu saɓa ba.”