Ɗan sanda ta kashe kansa a jihar Neja

Shafi’u Bawa wani ɗan sandan kwantar da tarzoma ya kashe kansa a Kantagora ta jihar Neja.

Bawa dake da muƙamin ASP  na aiki ne da  rundunar ƴan sandan kwantar da tarzoma runduna ta 61 an kuma gano shi yana reto ɗaure a igiya a cikin dakinsa da yammacin ranar Asabar.

Mahaifin ɗan sandan shi ne ya fara kwarmata faruwar lamarin bayan da ya gano gawar ɗan nasa inda ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin ƴan sanda na Kantagora..

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Wasiu Abiodun mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Neja ya ce  tuni aka fara bincike domin gano musabbabin mutuwar tasa.

Abiodun ya ce tuni aka miƙa gawar marigayin ga ƴan uwansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

More from this stream

Recomended