Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da jakar da ta bata mai dauke da sama da Naira miliyan 100.
A ƙarshen taron wa’azi na musamman da aka gudanar a Bauchi, Daraktan kungiyar Agaji ta farko na kasa Engr Mustapha Imam Sitti ya yabawa Kankia bisa gaskiyarsa.
Kungiyar JIBWIS reshen jihar Bauchi ta bayyana a shafinta na sada zumunta na Facebook cewa Kankia ya gano jakar kuma ba tare da bata lokaci ba ya kai rahoto ga ‘yan sanda.
Mai shi ya tabbatar da cewa babu abin da ya ɓace a cikin kuɗin.
Bisa la’akari da gaskiyarsa, kungiyar Izala ta karrama Kankia da lambar yabo da kuma daukar nauyinsa a aikin hajjin bana.
Ya kuma karbi Naira miliyan biyu daga hannun Hon. Abdulmalik Zannan Bangudu da motar bas daga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed domin fara harkar kasuwanci.